Tutar Rasha: Hukumomin Tsaro Za Su Yi Ganawar Sirri a Abuja Bayan Umarnin Tinubu

Tutar Rasha: Hukumomin Tsaro Za Su Yi Ganawar Sirri a Abuja Bayan Umarnin Tinubu

  • Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Najeriya, Hafsan tsaron Najeriya zai shiga ganawar gaggawa da shugabannin hukumomin tsaro
  • Janar Christopher Musa shi ya kira ganawar gaggawa bayan Shugaba Bola Tinubu ya ba su umarni kan masu zanga-zanga
  • Hakan bai rasa nasaba da daga tutocin kasar Rasha da masu zanga-zanga suke yi a fadin kasar cikin kwanakin nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa zai gana da shugabanin hukumomin tsaron kasar game da zanga-zanga.

Janar Christopher Musa ya dauki matakin ne bayan umarnin Bola Tinubu kan masu daga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zanga.

Umarnin Tinubu kan daga tutar Rasha ya tilasta shugabannin tsaro ganawa a Abuja
Hafsan tsaron Najeriya zai gana da hukumomin tsaro kan daga tutocin Rasha yayin zanga-zanga. Hoto: @DefenceinfoNG, @officialABAT.
Asali: Twitter

Hafsan tsaro zai yi ganawa kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jigon APC ya nemowa Tinubu mafita kan masu daga tutar Rasha

Daily Trust ta tattaro cewa za a yi ganawar a yau Talata 6 ga watan Agustan 2024 a birnin Abuja ana tsaka da zanga-zanga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ba a bayyana musabbabin ganawar ba amma hakan na da alaka da umarnin da Bola Tinubu ya ba su a jiya Litinin 5 ga watan Agustan 2024.

Tinubu ya nuna damuwa kan yadda zanga-zangar ta sauya salo tare da ba hukumomin tsaro umarnin daukar mataki, cewar Punch.

Zanga-zanga: Hukumomin da za su halarci ganawar

Wata majiya daga hedikwatar tsaron ta ce ganawar za ta kunshi shugabannin DSS da NIA da DIA da kuma bangaren 'yan sanda.

Sauran wadanda za su halarci ganawar sun hada hafsan sojojin kasa, Taoreed Lagbaja da na ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla da kuma na sama, Air Marshal Hassan Abubakar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da manyan hafsoshin tsaro ana tsaka da zanga zanga

Sannan akwai shugabannin hukumomin gidajen gyran hali da na Kwastam da na shige da fice da hukumar NSCDC da sauransu.

Majiyar ta ce za a fara ganawar a kowane lokaci daga yanzu idan Shugaba Tinubu ya ba da umarnin hakan.

Wannan na zuwa ne yayain da ake cigaba da zanga-zanga nuna damuwa kan halin ake ciki.

Tutocin Rasha: Jigon APC ya shawarci Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ya yi magana kan masu daga tutocin kasar Rasha inda ya shawarci Bola Tinubu kan haka.

Podar Johnson Yiljwan daga jihar Plateau ya shawarci Tinubu ya kira shugabannin masu zanga-zanga kan alakar tutocin rasha a lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.