An Kama Matasa 632 a Zanga Zanga, Kotu Ta Dauki Matakin Aika Wasu Zuwa Kurkuku
- Doka ta fara aiki a kan matasan da aka kama bisa zargin aikata laifuffuka daban-daban yayin gudanar da zanga-zanga a fadin jihar Kano
- Jami'an tsaro sun cafke akalla matasa sama da 600 da ake zargi da aikata sace-sace, tunzura jama'a da jawo tashe-tashen hankula a jihar
- A ranar Talata ne kotun tafi da gidanka da bangaren shari'a ya samar ya hukunta mutane 632 bisa laifuffuka da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kotun tafi da gidanka a jihar Kano ta dauki mataki a kan masu zanga-zanga 632 da aka kama bisa zargin lalata kadarorin jama'a.
Rundunar 'yan sandan Kano ta kama mutanen bisa zargin sata, lalata kadarorin jama'a da na gwamnati, tayar da hankula da gudanar da taro ba bisa ka'ida ba.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa manyan jami'an bangaren shari'a guda uku ne su ka jagoranci yanke hukuncin ta kotun tafi da gidanka a ofishin 'yan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tesa keyar masu zanga-zanga gidan kaso
Babban mai shari'a a kotun majistare, Ibrahim Mansur Yola da Hadiza Rabiu Bello da kuma Abba Muttaka-Dandago ne su ka jagoranci yanke hukunci a kotun.
Pulse Nigeria ta wallafa cewa kotu ta bayar da umarnin a adana wadanda aka kama a gidan gyaran hali da tarbiyya har zuwa ranar 19 Agusta, 2024 da za a ciba da shari'a.
Tun da fari, babban mai gabatar da kara na jiha, Salisu Tahir ya shaidawa kotun cewa ana zargin masu zanga-zangar da fasa shagunan jama'a tare da sace masu kayayyaki.
Matasa sun ki daina zanga-zanga
A wani labarin kun ji cewa kungiyar matasa ta Nigerian Patriotic Movement ta jaddada aniyarta na ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati.
Sakataren kungiyar ya ce ba za su janye daga akidarsu ba tun da Bola Tinubu ya ki duba kokensu ballanatana ya dauki matakin magance matsalolin da su ka yiwa kasa katutu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng