Gwamnatin Tarayya ta Dawo da Biyan Tallafin Fetur, Obasanjo Ya Fallasa Shirin Tinubu
- Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta dawo da biyan tallafin man fetur da ta cire
- Idan ba a manta ba, a shekarar 2023 lokacin jawabinsa na kama aiki, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur na take
- Sai dai a wata hira da aka yi da Obasanjo, ya ce tallafin da gwamnatin tarayya ta cire ya dawo saboda hauhawar farashin kayayyaki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa an dawo da tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya cire a shekarar 2023.
Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Tinubu ya dawo da biyan tallafin fetur din ne sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kasar ke fuskanta.
"An dawo da biyan tallafin fetur" - Obasanjo
A wata hira da aka yi da Obasanjo, ya caccaki yadda gwamnatin tarayyar ta cire tallafin ba tare da daukar wasu matakan daidaita lamura ba, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta aiwatar da wasu matakai kafin cire tallafin. Duk da hakan, ya bayyana cewa tallafin ya "dawo" saboda yawan hauhawar farashin kayayyaki.
Obasanjo ya soki yadda aka cire tallafi
Sahara Reporters ta ce Obasanjo ya soki yadda aka yi watsi da tsarin tallafin kwatsam a rana daya.
“Akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi. Ba za ka zo rana tsaka ka cire tallafin mai ba. Saboda hauhawar farashin kayayyaki, tallafin da aka cire a baya yanzu an dawo da shi."
- Olusegun Obasanjo.
Tinubu ya jaddada cire tallafin fetur
Ya kuma bayyana bukatar samun amincewar masu zuba jari a Najeriya, yana mai cewa, "Dole ne ku fita daga tsarin tattalin arzikin kasuwanci zuwa tattalin arzikin da ke sauyawa."
Legit Hausa ta ruwaito cewa dawo da biyan tallafin man fetur na daga cikin bukatun da masu zanga-zangar 'adawa da mummunar gwamnati' suka gabatarwa Shugaba Tinubu.
Sai dai a jawabin da shugaban kasar ya yi ranar Lahadi, ya ce lokaci ya kure da za a ce a dawo da tallafin, yana mai jaddada cewa tallafin fetur 'ya tafi kenan'.
Obasanja ya yi magana kan barayin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa Olusegun Obasanjo ya ce sama da kaso 80% cikin kaso 100% na ɗanyen man fetur na Najeriya sace shi ake yi.
Tsohon shugaban ƙasan ya ce yayin da adadin ɗanyen mai ya kai kusan ganga miliyan biyu a kowace rana, sama da ganguna miliyan 1.7 ake sacewa a kullum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng