Masu Zanga Zanga sun Ƙwace Motar Yaƙin Ƴan Sanda a Kaduna? Gaskiya ta Fito
- Rundunar 'yan sanda ta yi martani kan rahotannin da ake yadawa a shafukan intanet na cewa masu zanga-zanga sun kwace motar 'yan sanda
- Wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da masu zanga zanga suka yi rade-rade kan motar 'yan sanda a Kaduna
- Sai dai kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya ce wannan rahoto ko bidiyo da ake yadawa ba gaskiya bane, babu motarsu da aka kwace
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi magana kan wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya inda aka ga masu zanga-zanga sun yi dafifi saman wata motar yakin 'yan sanda.
Mafi akasarin wadanda ke wallafa bidiyon, sun shaida cewa masu zanga-zangar sun kwace motar yakin ne daga hannun jami'an 'yan sandan a jihar Kaduna.
Sai dai, a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan na kasa, Prince Olumuyiwa Adejobi ya fitar a shafinsa na X, an gano akasin ikirarin mutane.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyo: Matasa a kan motar 'yan sanda
Fitaccen mawakin Kudu, Charly Boy ya wallafa a shafinsa na X a jiya Litinin cewa masu zanga-zanga sun kwace motar 'yan sanda mai sulke.
Mawakin ya nuna damuwarsa kan yadda masu zanga-zangar suka yi dare-dare a kan motar yayin da yake nuna damuwarsa kan halin da kasar ke ciki.
Kalli bidiyon a kasa:
Masu zanga-zanga sun kwace motar 'yan sanda?
Sai dai a martanin da Prince Olumuyiwa Adejobi ya yi, ya ce ba a kwace motar sulke ta ‘yan sanda ba, sabanin faifan bidiyo da ake yadawa a yanar gizo.
Sanarwar kakakin rundunar ya ce masu zanga-zangar sun dare kan motar ne a lokacin da take kokarin barin wajen domin kai agaji a wani wuri na daban.
"Motar ta dawo sansanin da take, kuma tun kafin ta karasa masu zanga-zangar suka sauka tare da ranta a na kare. Babu wata motar 'yan sanda da masu zanga-zanga suka kwace a Kaduna."
- Inji kakakin rundunar.
Prince Olumuyiwa Adejobi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da wannan rahoto ko bidiyo da ake yadawa na cewa masu zanga-zanga sun kwace motar 'yan sanda a Kaduna.
Kaduna: Matasa na daga tutar Rasha
A wani labarin, mun ruwaito cewa zanga-zanga ta fara tsananta a jihar Kaduna yayin da aka ga wasu matasa suna daga tutar kasar Rasha duk a cikin adawa da tsadar rayuwa.
Wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da masu zanga-zangar ke balle kadarorin gwamnati suna awon gaba da su a yankin NEPA da ke jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng