Wani Gwamnan Arewa ya Rage Awannin Hana Fita, an Gurfanar da masu Zanga Zanga a Kotu
- Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya bayar da izinin sassauta dokar hana zirga-zirga ta sa’o’i 24
- Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa gwamnatin Katsina ta sanya dokar ne bayan da ta gano 'yan daba sun kwace zanga-zanga
- A zaman majalisar tsaron jihar da aka yi a yammacin Litinin, gwamnantin jihar ta sanar da awannin da aka mayar da zaman gidan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta amince da sake duba dokar hana zirga-zirga ta sa’o’i 24 da aka sanya a karamar hukumar Dutsinma da sauran kananan hukumomi 33 na jihar.
Mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe ya amince da sassauta dokar zaman gida a Dutsinma da kewaye bayan samun rahoton cewa an samu ingantaccen tsaro a yankin.
Katsina: An sassauta dokar hana fita
Malam Faruk Jobe ne ya amince da sassauta dokar, inda ya mayar da awannin hana fita daga karfe 7:00 na yamma zuwa karfe 7:00 na safe, inji sanarwar hadimin gwamna, Isa Miqdad a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mukaddashin gwamnan wanda ya ba da sabon umarnin ne a lokacin da ya jagoranci taron majalisar tsaro ta jihar a yammacin ranar Litinin.
Ya ba da umarnin hana duk wani nau'i na tarurrukan jama'a kuma ya jaddada ci gaba da aiwatar da dokar hana duk wani nau'in zanga-zanga a fadin jihar.
Malam Faruk Jobe yaba da yadda jami’an tsaro suka bi da ‘yan barandan da suka kwace zanga-zangar lumana domin aikata miyagun ayyuka a jihar.
An gurfanar da matasa a Katsina
Kwamitin tsaro na jihar ya sanar da kame wasu matasa da ake zarginsu da aikata laifukan tashe-tashen hankula da sace-sace da barnata dukiyoyin jama’a, inji rahoton Channels TV.
Jim kadan bayan kammala taron majalisar, sakataren gwamnatin Katsina, Barista Abdullahi Faskari ya ce tuni aka gurfanar da wasu daga cikin matasan da aka kama a gaban kuliya.
Barista Abdullahi Faskari ya ce ana tuhumar matasan ne da hada baki da tada hankulan jama’a, barna da kuma satar dukiyar jama'a.
Sakataren gwamnatin ya sake yin kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda, domin ba gwamnati da jami'an tsaro damar tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Katsina: An sanya dokar hana fita
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Katsina ta sanya dokar hana fita ta awanni 24 tare da haramta duk wani nau'i na zanga-zanga da taron jama'a .
Mukaddashin gwamnan jihar, Malam Faruk Jobe ne ya sanar da sanya dokar bayan barkewar rikici sakamakon zanga-zanga inda aka umarci jami'an tsaro su cafke masu kunnen kashi.
Asali: Legit.ng