Zanga-Zanga: Tinubu Ya Fadi Yadda Za a Ci Gajiyar Shinkafar N40,000, Ya Saka Ka’ida
- Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta shirya fara siyar da shinkafar N40,000 a kasar
- Gwamnatin ta ce ma'aikatan gwamnati ne za su ci gajiyar tallafin na shinkafa mai rahusa domin rage radadi ga al'umma
- Ma'aikatar ayyuka na musamman ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa inda ta ce za a tabbatar da adalci a rabon shinkafar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kammala shirin fara siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan N40,000 kacal a Najeriya.
Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne domin ragewa 'yan kasar halin kunci da suke ciki na mawuyacin hali a Najeriya.
Shinkafar N40,000: Tinubu ya fadi tsare-tsaren tallafin
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma'aikatar ayyuka na musamman ta fitar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce ma'aikatan gwamnati ne kadai za su ci gajiyar shinkafar inda aka ba su sharudan cike ka'ida domin samun tallafin.
Ma'aikatar ta ce biyan kudi da kuma rarraba shinkafar za a gudanar da su cikin tsari domin tabbatar da yin adalci, cewar TheCable.
Yadda za a ci gajiyar shinkafar N40,000
"A kokarin Gwamnatin Tarayya na ragewa al'umma radadin da ake ciki, gwamnati ta shirya fara siyar da shinkafa ga ma'aikata."
"Ina mai sanar da ku cewa za a siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan N40,000 ga ma'aikatan da suke da bukata a Abuja."
"Duk masu sha'awa za su cike bayanansu ta yanar gizo kamar haka: https://www.ohcsf.gov.ng domin samun damar cin gajiyar."
- Cewar sanarwar
'Yan Kano sun koka kan zanga-zanga
Kun ji cewa mazauna Kano da dama sun fara kokawa kan yadda aka fara rasa kayan masarufi dalilin zanga-zanga ada ake yi.
Jama'a da dama suka ce kulle kasuwanni da ake cigaba da yi ya tilasta karewar kayan masarufi a shaguna da yawa.
Hakan bai rasa nasaba da cigaba da zanga-zanga da ake yi da kasuwanni suka kasance a kulle na tsawon kwanaki.
Asali: Legit.ng