Zanga-Zanga: Yadda Dan Sanda Ya Bindige Matashi a Bainar Jama’a, an Shiga Firgici
- Mutane da dama sun shiga firgici bayan wani dan sanda ya bindige wani matashi mai zanga-zanga har lahira a gaban jama'a
- Lamarin ya faru ne a garin Azare da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi yayin da ake cigaba da zanga-zanga a kasar
- Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya dokar hana fita a karamar hukumar bayan barkewar rigima tare da lalata dukiyoyin al'umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Jami'an tsaro sun bindige wani mai zanga-zanga a jihar Bauchi cikin wani irin yanayi mai ban tausayi.
Lamarin ya faru ne a Azare da ke karamar hukumar Katagum a jihar a gaban sakatariyar karamar hukumar.
Zanga-zanga: Rikici a barke a jihar Bauchi
Daily Trust ta tattaro cewa a cikin wani bidiyo an gano yadda 'yan sanda suka fafata da masu daga tutocin Rasha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano yadda jam'ian tsaro har guda uku suka kwantar da matashin a kasa inda suka yi ta dukansa.
Daga bisani wani daga cikin jami'an tsaron ya matso kusa da shi ya nuna bindigarsa gare shi tare da harbinsa nan take.
Mutane da dama da ke wurin sun yi ihu yayin da dan sandan bayan ya yi harbi ya juya ya cigaba da tafiya abinsa, cewar Channels TV.
Wani mazaunin Azare da ya bukaci boye sunansa, ya ce marigayin na daga cikin miyagu da 'yan sandan suka kama.
Zanga-zanga: Gwamnati ta sanya dokar kulle
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya dokar kulle na tsawon awanni 24 bayan barkewar rikici a karamar hukumar Katagum.
A ranar Litinin 5 ga watan Agustan 2024 an cinnawa wani bangare na sakatariyar karamar hukumar wuta.
Masu zanga-zanga sun lalata ababan hawa tare da fasa gidan tsohon mataimakin gwamna, Baba Tela tare da sace-sace.
Abin a ya faru a gidan Buhari
Kun ji cewa Masarautar Daura ta yi magana bayan jita-jitar cewa masu zanga-zanga sun zagaye gidan sarkin da na Muuhammadu Buhari.
An ruwaito cewa wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a gidan tsohon shugaban kasa da kuma Sarkin Daura a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng