Zanga Zanga: Gwamnatin Kano ta Ɗauki Matakai 6, Ta Yi Magana kan Ɗaga Tutar Rasha

Zanga Zanga: Gwamnatin Kano ta Ɗauki Matakai 6, Ta Yi Magana kan Ɗaga Tutar Rasha

  • Gwamnatin ta ce tana da cikakken rahoto kan yadda zanga-zangar ta jawo asarar rayuka, lalata dukiya, sace kayan jama'a da dai sauran su
  • A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin Kano ta dauki matakai shida domin magance matsalar masu zanga-zangar
  • Daga cikin matakan da aka dauka akwai bude cibiyoyin bayar da horo ga matasa kan sana'o'i, yayin da ta yi magana kan daga tutar Rasha

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce ta nuna takaicinta kan yadda wasu yan daba suka kwace zanga-zangar lumana suka mayar da ita ta ta'addanci.

Gwamnatin ta ce tana da cikakken rahoto kan yadda zanga-zangar ta jawo asarar rayuka, lalata dukiya, sace kayan jama'a da dai sauran su.

Kara karanta wannan

Kaduna, Zariya: Gwamna ya sanya dokar hana fita ta awa 24, an ba jami'an tsaro umarni

Gwamnatin Kano ta yi magana kan daga tutar rasha da ake yi a lokacin zanga-zanga
Kano: Gwamnati ta dauki wasu matakai da za su iya magance matsalar masu zanga-zanga. Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Gwamnatin Kano ta magantu kan zanga-zanga

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf ya fitar, wadda Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ruwaito Gwamna Abba Yusuf yana nuna takaicinsa kan yadda wasu 'yan siyasa marasa kishi' suka kuduri aniyar haddasa rikici a Kano domin manufarsu ta siyasa.

Gwamnan ya tabbatar da cewa za a hukunta duk wanda aka kama da tayar da zaune tsaye a jihar yayin da yake ci gaba da bibiyar abubuwan da ke faruwa, a cewar sanarwar.

Gwamnatin Kano ta dauki matakai 6

Sai dai duk da hakan, sanarwar ta ce gwamnati ta dauki wasu matakai da suka shafi tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummarta, wadanda take son jama'a su mayar da hankali kansu.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga na daga tutar Rasha a Kaduna, an fara awon gaba da kayan jama'a

1. Hukunta masu tayar da zaune tsaye

Sanarwar ta ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da hukunta sama da mutane 600 da aka kama bisa zargin sun tayar da zaune tsaye a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar.

An ce za a fara hukunta wadanda ake zargin ne daga yau Litinin, 5 ga watan Agustan 2024.

2. Za a bude cibiyoyin horas da matasa

Gwamnan Kano ya ba da umarnin dawo da koyarwa a cibiyoyin horas da matasa sana'o'in dogaro da kansu, inda za a yiwa dubunnan matasa rijista domin su zamo masu dogaro da kansu.

3. Cibiyar gyaran tarbiya za ta fara aiki

Cibiyar gyaran tarbiya ta Kano da ke Kiru ta za ta fara horar da matasan da ke fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi nan da wani lokaci.

4. An kafa kwamitin binciken zanga-zanga

Gwamna Abba Yusuf zai kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai binciki kashe-kashe da barnata kadarori na gwamnati da na jama’a da aja yi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Bayan rasa rayuka, masu zanga zanga sun fara alkunutu a Kano

Sanarwar ta ce gwamnan ya dauki matakin ne bayan samun kiraye-kiraye daga 'yan Najeriya, kasashen ketare, kungiyoyin kare 'yancin dan Adam, sarakuna da malamai.

5. Neman hadin kan al'ummar Kano

Gwamnati ta yi kira ga mutanen Kano da su goyi bayan wadannan matakai ta hanyar samar da bayanai masu amfani ga kwamitin binciken wanda za a kafa nan gaba kadan.

6. Gwamnati ta magantu kan daga turar Rasha

A karshe, sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Yusuf ba ta da alaka kai tsaye ko ta fakaice da duk wasu masu zanga-zanga musamman masu daga tutar wata kasar waje.

Kaduna: Masu zanga-zanga na daga turar Rasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan jihar Kaduna inda aka gansu suna daga tutar kasar Rasha.

Wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane ke daga tutar kasar wajen yayin da kuma wasu ke sace kadararorin gwamnati da ma na al'umma gama gari.

Kara karanta wannan

Zargin kashe masu zanga zanga: Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin bincikar jami'an tsaro

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.