Tsadar Rayuwa: Wasu Abubuwa 5 da Suka Ja Hankali daga Fara Zanga Zanga Zuwa Yau

Tsadar Rayuwa: Wasu Abubuwa 5 da Suka Ja Hankali daga Fara Zanga Zanga Zuwa Yau

  • Tun ranar 1 ga watan Agusta al'ummar Najeriya suka fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a kusan dukkan Najeriya
  • A cikin kwanaki biyar da aka shafe ana cigaba da zanga zangar an samu muhimman abubuwan da suka ja hankalin al'umma
  • A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku manyan abubuwa biyar da suka ja hankalin yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Al'ummar Najeriya na cigaba da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a kusan dukkan fadin Najeriya.

Yayin da aka yi kwana biyar ana zanga zangar, abubuwan da suka ja hankali da dama sun faru a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Zanga zanga ta birkice, matasa sun toshe hanyoyi

tutar rasha
Muhimman abubuwa da suka faru a lokacin zanga zanga a Najeriya. Hoto: Mudassir Ibrahim
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku abubuwa biyar masu muhimmanci da suka faru kuma suka ja hankalin al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Dandazon jama'a wajen zanga zanga

Yan Najeriya da dama sun zuba ido suga ko za a samu mutane da dama da za su halarci filayen zanga zanga a faɗin Najeriya musamman yadda malamai da gwamnati suka yi gargadi.

Abin da ya ja hankali shi ne jama'a sun fito da dama musamman a jihohin Arewa inda hakan ya rika haifar da tattaunawa a kafafen sada zumunta.

2. Tunkarar gidan Muhammadu Buhari

Masu zanga zanga a Daura da ke jihar Katsina sun tunkari gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari suna ihu.

Hakan ya ja hankalin masu hasashe da dama a fadin Najeriya inda suke ganin cewa a yanzu kwarjinin tsohon shugaban kasar ya ragu.

Kara karanta wannan

Ana cikin zanga zangar lumana an jefa Filato cikin matsala

3. Hadin kan mutane a Filato

Wani abin da ya ja hankalin mutane shi ne hadin kan da aka samu tsakanin al'ummar Musulmi da Kirista a yayin zanga zanga a jihar Filato.

Tattaunawa a kafafen sada zumunta ta karkata kan jihar Filato ganin ba a samu barkewar rikicin addini saboda zanga zangar ba.

4. Jawabin shugaba Bola Tinubu

Yayin da aka yi kwanaki uku da fara zanga zangar, Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi magana ga yan Najeriya a ranar Lahadi.

Sai dai maganar da ya yi ta ja hankulan al'umma sosai ciki har da manyan yan siyasa, kungiyoyi da masu zanga zangar.

5. Yin amfani da tutar kasar Rasha

Wani abu da ya ja hankalin al'umma shi ne yadda wasu masu zanga zangar ke amfani da tutar kasar Rasha maimakon tutar Najeriya.

Har zuwa wanna lokaci ba a samu wani sahihin bayani kan dalilin masu anfani da tutar Rashan ba duk da cewa jami'an tsaro sun kama wani mai dinka tutar a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yadda yan sanda suka hallaka Bayin Allah lokacin zanga zanga a jihar Kano

Afenifere ta caccaki Bola Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cigaba da shan suka kan kalaman da ya yi a ranar Lahadi game da masu zanga zanga.

Babbar kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi Allah wadai da kalaman da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kan masu zanga zangar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng