Legas: 'Yan Daba Sun Kai Mamaya kusa da Ofishin Gwamna, An Tarwatsa Masu Zanga Zanga
- Wasu masu zanga-zanga a kusa da ofishin gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da ke kan titin Alausa sun ranta a na kare
- An ruwaito cewa masu zanga-zangar sun tarwatse tare da gudun ceton rai bayan da 'yan daba suka farmake su da makamai
- Wata majiya ta ce jami'an tsaron da aka jibe a kusa da wajen sun juya baya yayin da 'yan daban ke fatattakar masu zanga-zangar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - 'Yan daba sun fatattaki wasu daga cikin masu gudanar da zanga-zanga a kan titunan Alausa, hedikwatar gwamnati a jihar Legas.
An ce ofishin Gwamna Babajide Sanwo-Olu yana a Aluasa, inda masu zanga-zangar suka yi dafifi bayan kin zuwa filin shakatawa na Freedom dake Ojota, inda kotu ta amince da gudanar da zanga-zangar a Legas.
Sai dai kuma, da misalin karfe 12:00 na rana, ‘yan daba sun farmaki masu zanga-zangar da sanduna, adduna da makamai daban-daban inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yan daba sun farmaki masu zanga-zanga
Ganin irin wahalar da za su iya sha, ya tilasta masu zanga-zangar ranta a na kare idan suka tarwatse kowa ya kama gabansa yayin da 'yan daban suka rika bin bayansu
An ruwaito cewa jami'an tsaron da aka girke a wajen sun yi biris kamar ba su ga abin da ke faruwa ba yayin da masu zanga-zangar ke gudun ceton rai.
Wannan dai na zuwa ne awanni 24 bayan wasu 'yan daba sun fatattaki masu zanga-zanga daga filin shakatawa na Freedom jim kadan bayan jawabin Shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya aika sako ga 'yan Najeriya
A ranar Lahadi ne Legit Hausa ta ruwaito cewa Bola Tinubu ya yi kira ga matasa a fadin kasar da su kawo karshen zanga-zangar yayin da gwamnatinsa ta dauki matakan gyara.
Shugaban kasar wanda ya ce zanga-zangar da ake yi ta rikide zuwa tashin hankali ya ce ba zai zura ido wasu 'yan siyasa su tarwatsa kasar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng