Fargabar Wawaso: An Dauki Mutum 800 Domin Tsare Kasuwar Kano Daga Masu Zanga Zanga

Fargabar Wawaso: An Dauki Mutum 800 Domin Tsare Kasuwar Kano Daga Masu Zanga Zanga

  • Fargabar yadda 'yan daba da miyagu su ka koma sace-sace yayin zanga-zanga ya sa mahukuntan kasuwar Dawanau daukar mataki
  • Kasuwar Dawanau da daga cikin manyan kasuwannin Afrika ta Yamma da ake hada-hadar hatsi har zuwa kasashen wajen Najeriya
  • Shugaban kungiyar Dawanau Development Association ya bayyana cewa yanzu haka an dauki mutane 800 domin ba kasuwar kariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar 'yan kasuwar hatsi ta Dawanau da ke karamar hukumar Tofa a Kano sun dauki matakin kare dukiyoyinsu da ke cikin kasuwar.

Wannan ya biyo bayan karuwar samun labarin fashe-fashen shaguna da wuraren da aka ajiye kaya tare da sace su a sassan Kano.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Bayan rasa rayuka, masu zanga zanga sun fara alkunutu a Kano

Kasuwa
An dauki mutum 800 domin ba wa kasuwar Dawanau kariya Hoto: Samuel Alabi/Aminu Abubakar
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kungiyar Dawanau Development Association, Muntaka Isa, ya bayyana cewa an dauki matasa 800 aikin tabbatar da an ba wa kasuwar su kariya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Ana tsare kasuwar Dawanau

Shugaban kungiyar Dawanau Development Association, Muntaka Isa ya ce akwai hadin gwiwa tsakanin jami'an tsaro soja, 'yan sanda da bijilanti domin bayar da tsaro a kasuwar.

Ya ce za su yi aiki tukuru domin raba kasuwar da satar masu fakewa da zanga-zanga, kamar yadda aka rika gani a wasu sassan jihar.

Muntaka Isa ya ce an dauki 'yan sa kai 400 domin taimakawa jami'an tsaron jihar wajen tabbatar da ba a yi masu barna ba.

An tsaurara tsaro a Dawanau gabanin zanga zanga

A bayaninsa ga Legit, shugaban kungiyar Dawanau International grains market association, Mustapha Yusuf Maikalwa ya bayyana cewa dama kafin yanzu an tsaurara tsaro.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sandan Kano sun tashi tsaye, an fara bin gida gida neman kayan sata

Ya ce su na sane da illar da za a iya yiwa 'yan kasuwar, wanda haka ne ya sa su ka dauki matakan tun da fari.

Masu zanga zanga sun sake fitowa

A baya mun ruwaito cewa fusatattun 'yan Najeriya sun yi biris da barazanar 'yan daba wajen fitowa domin ci gaba da gudanar da zanga-zanga a rana ta biyar.

Masu zanga-zangar da su ka fito bayan 'yan daba sun koresu a Legas na ganin jawaban shugaban kasa, Bola Tinubu bai bayyana wani sassauci garesu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.