Masu Zanga Zanga na Daga Tutar Rasha a Kaduna, an Fara Awon gaba da Kayan Jama'a

Masu Zanga Zanga na Daga Tutar Rasha a Kaduna, an Fara Awon gaba da Kayan Jama'a

  • Zanga-zanga ta fara tsananta a jihar Kaduna yayin da aka ga wasu matasa suna daga tutar kasar Rasha duk a cikin adawa da tsadar rayuwa
  • A yankin titin NEPA kuwa, an ga wasu 'yan daba da suka saje da masu zanga-zangar suna fasa gine-ginen jama'a suna kwaso dukiyarsu
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da zanga-zangar 'adawa da mummunar gwamnati' ta shiga rana ta biyar bayan da aka fara ta a ranar 1 ga Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Masu zanga-zanga sun mamaye manyan tituna a Kaduna, kamar yadda bidiyo daban daban ya nuna yadda zanga-zangar ta tsananta a kwaryar jihar.

Kama daga titin NEPA, zuwa kan titin Ahmadu Bello har ya kai ga babbar gadar Kawo, daruruwan matasa ne rike da tutocin Najeriya suna ihun 'Bama yi," "Mun gaji da wahala" da sauransu.

Kara karanta wannan

Legas: 'Yan daba sun kai mamaya kusa da ofishin gwamna, an tarwatsa masu zanga zanga

Masu zanga-zanga na daga tutar Rasha a Kaduna
Zanga-zanga ta tsananta a Kaduna, matasa na daga turar Rasha. Hoto: @Miniko_jnr
Asali: Twitter

Masu zanga-zanga sun saci kayan jama'a

Wani faifan bidiyo da Channels TV ta wallafa ya nuna lokacin da wasu bata gari daga cikin masu zanga-zangar suka rika balle kadarorin gwamnati suna awon gaba da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan talabijin din ya yi ikirarin cewa abin ya faru ne a titin NEPA idan aka rika ganin matasa suna fasa gine-ginen gwamnati da na jama'a suna satar kaya.

"Yan daba sun farmaki gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu a kewayen titin NEPA da ke Kaduna inda suka yi awon gaba da kayayyaki," a cewar rahoton.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu zanga-zanga na daga tutar Rasha

Har ila yau, Channels TV ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda wasu matasa masu zanga-zanga ke daga turar kasar rasha, duk a cikin adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kaduna, Zariya: Gwamna ya sanya dokar hana fita ta awa 24, an ba jami'an tsaro umarni

Ba wannan ne karon farko da aka ga masu zanga-zanga na daga tutar Rasha ba, ko a jihar Kano irin hakan ta faru, lamarin da ya jawo cece kuce, inda wasu ke ganin hakan cin amar kasa ne.

Daya daga cikin masu zanga-zangar, Auwalu Idi, ya shaida wa jaridar This Day cewa:

“Mun gwammace mu mutu da harsashi da mu mutu da yunwa, ba za mu iya zama a gida mu mutu da yunwa ba.”
"Muna daga tutar Rasha ne saboda mun yi imanin Tinubu yana mulki ne bisa tsarin da Bankin Duniya, Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Amurka suka dora shi a kai."

Kalli bidiyon a kasa:

Zanga-zanga: An kona ofishin KASTLEA

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu zanga-zanga sun je ofishin hukumar KASTLEA da ke jihar Kaduna inda suka cinna masa wuta.

An ce masu zanga zangar sun kuma wawushe dukiyar jama'a da ke a cikin ofishin tare da fasa gidaje da ofisoshin makotan hukumar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.