Zargin Kashe Masu Zanga Zanga: Gwamnatin Kano za ta Kafa Kwamitin Bincikar Jami’an Tsaro

Zargin Kashe Masu Zanga Zanga: Gwamnatin Kano za ta Kafa Kwamitin Bincikar Jami’an Tsaro

  • Gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin shari'a da zai binciki yadda jami'an tsaro suka gudanar da ayyukansu a lokacin zanga-zanga a jihar
  • An ce kwamitin zai kuma yi kwakkwaran bincike kan yadda wasu 'yan barandan siyasa da aka yo hayarsu suka sace dukiyar jama'a a jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka yi zargin cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun kashe matasa a wasu sassa na jihar lokacin zanga-zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin Kano ta yi magana kan abubuwan da suka faru a jihar sakamakon zanga-zangar 'adawa da mummunar gwamnati' da ake yi a fadin kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe matasa da dama a Kano yayin da a hannu daya kuma 'yan daba suka fasa shagunan jama'a tare da sace kayayyaki.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

Gwamnatin Kano za ta yi bincike kan abubuwan da suka faru lokacin zanga-zanga a jihar
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai binciki ayyukan jami'an tsaro lokacin zanga-zanga. Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Mai tallafawa Gwamna Abba Yusuf ta fuskar kafofin sada zumunta Abduallahi I. Ibrahim ya sanar a shafinsa na X cewa gwamnatin Kano za ta binciki ayyukan masu zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: An kafa kwamitin bincike a Kano

A sanarwar da ya fitar a ranar 4 ga Agustan 2024, Abdullahi Ibrahim ya ce gwamnatin Kano za ta kafa kwamitin shari'a da zai yi cikakken bincike kan ayyukan jami'an tsaro a lokacin zanga-zangar.

Hakazalika, sanarwar ta ce kwamitin da za a kafa zai kuma binciki irin barnar da wasu bata gari da aka yi hayarsu suka tafka a fadin jihar a ranakun da ake zanga-zangar.

Ga abin da sanarwar Abdullahi ke cewa:

"Gwamnatin Jihar Kano za ta kafa kwamitin bincike na shari’a domin yin cikakken bincike kan yadda hukumomin tsaro ke gudanar da ayyukansu da kuma barna da ake zargin ‘yan barandan haya suka tafka a lokacin zanga-zangar 'adawa da mummunar gwamnati'."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Tinubu ya dauki alkawari 1 yayin da ya fallasa shirin wasu 'yan siyasa

An zargi jami'an tsaro da kashe matasa

Fitaccen dan jarida, Jaafar Jaafar ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ana zargin 'yan sanda da kashe matasa yankunan Kurna/Rijar Lemo da Ƙofar Nassarawa a jihar Kano.

Jaafar Jaafar ya ce ya samu sakonni bila adadin daga wadanda abin ya faru a gaban idanunsu, inda ya bukaci gwamnatin Kano ta yi bincike tare da hukunta jami'an tsaron.

A cewar dan jaridar:

"Yakamata a hukunta jami’an tsaro da suka kashe waɗannan mutane, cikinsu har da ƙanan yara."

Masu zanga-zanga sun yi barna a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa ma'aikatar shari'a ta Kano ta tafka asara bayan masu zanga-zanga sun kutsa cikinta tare da sace muhimman abubuwa da kona dukiyoyin jama'a.

Daga cikin abubuwan da aka sace akwai takardun tuhuma, kudi da bindigu da aka kama a matsayin shaida daga hannun masu garkuwa da mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.