Zanga Zanga: Kwankwaso Ya Fadi Wanda Zai Dauki Alhakin Barnar da Aka Yi a Kano

Zanga Zanga: Kwankwaso Ya Fadi Wanda Zai Dauki Alhakin Barnar da Aka Yi a Kano

  • Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya fito ya yi magana asarar rayuka da dukiyoyin da aka samu sakamakon zanga-zangar lumana a jihar Kano
  • Jigon na jam'iyyar APC, ya buƙaci a ɗora alhakin duk abin da ya faru a kan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, saboda shi ya ce mutane su fito zanga-zanga
  • Kwankwaso wanda tsohon kwamishina ne ya yi kira ga waɗanda lamarin ya shafa da su je kotu domin neman a biya su diyya kan asarar da suka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso, ya yi magana kan rikicin da aka samu a Kano sakamakon zanga-zanga.

Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ɗorawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, alhaki kan ɓarna, asarar rayuka da dukiyoyin da aka samu sakamakon a zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Duk da barkewar rikici, gwamna ya fadi dalilin kin kulle mutane a guda

Musa Iliyasu Kwankwaso ya caccaki Gwamna Abba
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukaci a nemi diyya wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Musa Sale Danzaria
Asali: Facebook

Kwankwaso ya yi magana kan zanga-zanga

Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne jiya a Kano a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan zanga-zangar a birnin Kano, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yabawa Rabiu Musa Kwankwaso bisa kiran da ya yi na kada mutane su fito kan tituna domin yin zanga-zanga, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Kano: Kwankwaso ya caccaki Gwamna Abba

Ya yi zargin cewa gwamnan jihar ne ya yi kira ga jama’a da su fito su yi zanga-zanga har ma ya ce zai jira su a gidan gwamnati domin karɓar kokensu, ya kuma yi alƙawarin miƙa shi ga shugaban kasa domin ɗaukar mataki.

"Gwamna ne ya kamata ya ɗauki alhakin rikici da ɓarnatar dukiyar da fusatattun masu zanga-zanga da ke jin yunwa suka yi."
"A jihar Kano, gwamnan ne ya yi kira ga mutane da su fito su yi zanga-zanga. Yanzu da aka kashe mutane aka lalata dukiyoyi sai ya ɗauki alhaki ya biya diyya."

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi ya bayyana mummunar illar da zanga zanga ta jawo a Kano da Arewa

"Ya kamata waɗanda rikicin ya ritsa da su, su samu ƙwararrun lauyoyi, su je kotu domin neman diyya daga jiha."
"Saboda gwamnan ne ya ce su fito su yi zanga-zanga duk da mai gidansa Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira da kada mutane su yi zanga-zanga. Dole ne ya biya diyya."

- Musa Iliyasu Kwankwaso

Sanusi II ya magantu kan sata a zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi Allah wadai da mummunan halin sace-sace da aka yi a lokacin zanga-zanga.

Sarkin Kano na 16, mai martaba Sanusi II ya nemi jama'ar jihar su gaggauta mika bayanan kayan sata da aka dauka lokacin zanga-zanga ga ƴan sanda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng