An Shiga Fargaba, Masu Zanga Zanga Sun Saci Bindigogi da Kudi a Kano
- Yayin da aka shiga kwana na biyar na gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan, an fara gano asarar da masu fitowa nuna fushinsu su ka jawo
- Ma'aikatar shari'a ta jihar Kano ta gano yadda masu zanga-zangar da su ka afka mata su ka tafka barna ta hanyar yin sace-sace da kone-kone
- Daga cikin abubuwan da aka sata akwai bindigu da aka kwato daga hannun wasu da ake zargi da aikata mugayen laifuka a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Ma'aikatar shari'a ta Kano ta tafka asara bayan masu zanga-zanga sun kutsa cikinta tare da sace muhimman abubuwa da kona dukiyoyin jama'a. Daga cikin abubuwan da aka sace akwai takardun tuhuma, kudi da bindigu da aka kama a matsayin shaida daga hannun masu garkuwa da mutane.
Jaridar The Punch ta wallafa cewa jami'in hulda da jama'a na babbar kotun jiha, Baba Ibrahim ne ya tabbatar da sace-sacen a Kano.
Masu zanga-zanga sun tafka barna
Kakakin ma'aikatar shari'a ta Kano, Baba Ibrahim ya bayyanawa manema labarai cewa an fara binciken wadanda su ka kutsa ma'aikatar tare da sace muhimman abubuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Naija News ta tattaro cewa a ranar Alhamis ne bara-gurbin cikin masu zanga-zanga su ka shiga ma'aikatar tare da sace kudi masu yawa da kona ababen hawa.
Ana binciken masu zanga-zanga a Kano
Wannan shi ne karon farko da ma'aikatar shari'a ta Kano ta taba fuskantar makamanciyar asarar da aka gani a lokacin zanga-zanga
Baba Ibrahim ya ce tuni aka kafa kwamitin bincike domin gano ainihin wadanda su ka yi sace-sacen domin a hukunta su.
'Yan daba sun tarwatsa masu zanga-zanga
A wani labarin kun ji cewa 'yan daba sun tarwatsa masu gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a Legas.
'Yan daban sun bayyana dalilin tarwatsa masu zanga-zangar da cewa shugaban kasa ya riga ya yiwa mutane jawabi, saboda haka kowa ya koma gidansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng