Ba a Gama Bude Kano ba, Wani Gwamna Ya Sake Sanya Dokar Hana Fita a Arewa
- Gwamnatin Plateau ta ɗauki matakin sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a wasu sassan jihar bayan wasu ɓata gari sun tafka ɓarna
- Gwamnan jihar, Mai girma Caleb Mutfwang ya sanya dokar a birnin Jos da Bukuru biyon bayan sace-sacen da wasu ɓata gari suka yi
- A cikin sanarwar da aka fitar kan sanya dokar, an bayyana cewa dokar nan za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi da daddare
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a birnin Jos da Bukuru.
Gwamnan ya bayyana cewa an sanya dokar ne biyo bayan samun rahotannin ƴan daba sun yi sace-sace a unguwar titin Bauchi da mahaɗar Zololo.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Gyang Bere, ya fitar a ranar Lahadi da daddare, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka sanya dokar hana fita a Plateau?
Gyang Bere ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin inganta tsaro da zaman lafiyar jama'a, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
"A wani mataki na inganta harkokin tsaro da zaman lafiyar jama’a, gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Jos/Bukuru, wacce za ta fara aiki daga daren ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024."
"Gwamna Mutfwang, tare da tuntuɓar hukumomin tsaro na jihar, ya ɗauki wannan matakin ne bayan nazari kan ayyukan ɓata gari da suka yi amfani da zanga-zangar da aka gudanar a fadin ƙasar nan wajen aikata ɓarna kan jama'a.
"Gwamnan ya ƙara da cewa, waɗannan ɓata gari ɗauke da wuƙa, adduna, da sauran muggan makamai, sun kutsa cikin shaguna da gidajen cin abinci da ke kan hanyar Bauchi da mahaɗar Zololo, inda suka sace kayan abinci da sauran kayayyaki."
- Bere Gyang
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya gargadi masu shirin ƙara aikata ɓarna kan jama'a da su gaggauta fasawa ko kuma su fuskanci fushin doka.
Tsohon minista ya fito zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya shiga zanga-zangar da matasa ke yi a birnin Jos na jihar Plateau.
Tsohon ministan na gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya shiga zanga-zangar ne wacce ake gudanarwa kan halin ƙunci da wahalar da ake fama da ita a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng