An Gano Abin da Ya Faru da Masu Zanga Zanga Suka Nufi Gidan Buhari da Sarkin Daura
- Yayin da aka yada jita-jitar cewa wasu masu zanga-zanga sun kai hari gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, an gano gaskiya
- Masarautar Daura ta yi martani kan lamarin inda ta musanta taba gidan Buhari ko kuma na Sarkin Daura a jihar Katsina
- Masarautar ta ce babu wanda ya taba gidajen biyu hasalima wucewa kawai suka yi yayin da suke zanga-zangar ta su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Masarautar Daura ta yi magana bayan jita-jitar cewa masu zanga-zanga sun dira gidan Sarkin garin da na Muuhammadu Buhari.
An ruwaito cewa wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a gidan tsohon shugaban kasa da kuma Sarkin Daura a jihar Katsina.
Zanga-zanga: An karyata kai hari gidan Buhari
Kakakin Sarkin Daura, Usman Ibrahim Yaro ya musanta cewa matasan sun taba gidajen Buhari da na sarkin, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaro ya ce masu zanga-zangar ba su yi ko kusa da gidajen ba sun wuce ne kawai ta wurin yayin da suke nuna damuwa kan halin kunci.
Ya ce duk da matasan sun farfasa allunan hoton 'yan siyasa a Daura amma ba su taba na kofar gidan Buhari da na Sarkin ba.
Masarautar Daura ta yi magana kan zanga-zanga
"Masu zanga-zanga ba su taba gidan Buhari da na Sarkin Daura ba labarin da ake yadawa karya ne kawai."
"Ba a samu matsala a zanga-zanga da aka yi ba a Daura, mutane yawanci sun yi ta bukukuwan aure yayin dokar kulle da aka yi."
- Usman Ibrahim Yaro
Yaro ya ce faifan bidiyon da ake yadawa ba gaskiya ba ne saboda an yi zanga-zanga a Daura amma babu tashin hankali.
Tinubu ya magantu kan tallafin mai
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan dawo da tallafin man fetur da ya jefa al'umma cikin kunci a Najeriya.
Shugaban ya ce cire tallafin ya zama dole duk da ya san halin kunci da hakan ya jefa 'yan Najeriya a ciki na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng