Tinubu Ya Fadi Dalilinsa Na Cire Tallafin Man Fetur, Ya Yi Jawabi Dalla Dalla
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana amfanin cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje
- Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya ɗauki matakin cire tallafin man fetur ɗin ne domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan
- Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya yiwa ƴan Najeriya kan zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilinsa na cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen wajen.
Shugaban ƙasan ya ce ya cire tallafin man fetur ɗin ne domin ya bunƙasa tattalin arziƙi da kawo ci gaba a ƙasa.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da yake jawabi dangane da zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Tinubu ya cire tallafin man fetur?
Tinubu ya ce ya ɗauki matakin cire tallafin man fetur da kawar da mabambantan farashin canjin kuɗaɗen ƙasar waje domin kawo ƙarshen ribar da masu fasa ƙwauri da masu neman bashi suke samu.
Tinubu ya ƙara da cewa matakin ya kawo ƙarshen tallafin da Najeriya take ba ƙasashe makwabtanta wanda ke ƙoƙarin durƙusar da tattalin arziƙinta, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
"Duka shekara ɗaya da ta wuce, ƙasarmu Najeriya, ta kai matakin da ba za mu iya ci gaba da amfani da mafita ta wucin gadi ba domin magance matsalolin da suka daɗe suna yi mana katutu, saboda goben mu."
"Waɗannan matakan da na ɗauka sun zama wajibi idan har dole sai mun sauya shekaru da dama da aka kwashe ana yiwa tattalin arziƙin ƙasar nan ɓarna wanda hakan bai amfane mu da komai ba."
- Bola Tinubu
Tinubu ya gargaɗi masu nuna ƙabilanci
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriyar da yake son ginawa ba ta da wurin nuna bambancin ƙabilanci.
Shugaban ƙasan ya yi gargaɗin cewa masu yiwa wasu ƙabilu barazana a wasu yankuna na ƙasar nan doka za ta yi aiki a kansu.
Asali: Legit.ng