Tinubu Ya Manta da Musabbabin Zanga Zanga, Ya Tura Sako ga Iyalai a Najeriya

Tinubu Ya Manta da Musabbabin Zanga Zanga, Ya Tura Sako ga Iyalai a Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana damuwa kan yadda aka samu rasa rayuka da dukiyoyi yayin zanga-zanga
  • Tinubu ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin samar da zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'umma
  • Shugaban ya jajantawa iyalai da ƴan uwan wadanda suka rasa rayukansu inda ya bukaci a dakatar da zanga-zanga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya yayin da ake cigaba da zanga-zanga.

Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu da kuma samun raunuka yayin zanga-zangar da ake yi.

Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu a zanga-zanga
Bola Tinubu ya bukaci matasa su dakatar da zanga-zanga. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya roki matasa kan zanga-zanga

Shugaban ya bayyana haka ne a yau Lahadi 4 ga watan Agustan 2024 da hadimansa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Jawabin Tinubu ya fara tasiri, matasa sun janye zanga zanga a birnin Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya bukaci matasa da su janye daga zanga-zanga domin samun damar tattaunawa da su.

Ya ce a matsayinsa na shugaban kasa hakki ne a kansa ya samar da zaman lafiya da kare dukiyoyin al'umma.

Tinubu ya kaɗu da rasa rayuka a zanga-zanga

"Na ji zafin abubuwan da suka faru a Kano da Kaduna da Jigawa da Borno da sauran jihohi dalilin zanga-zanga."
"Ina jajantawa iyalai da ƴan uwan wadanda suka mutu yayin zanga-zangar, dole mu dakatar da zubar da jini da tarwatsa arzikin kasa."
"Hakkina ne na samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Najeriya ba ki daya kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba ni dama."

- Bola Tinubu

Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta zuba ido kan wasu tsiraru masu mugun nufi a siyasance su tarwatsa Najeriya ba.

Kara karanta wannan

"Tinubu ya gama jawabi": Miyagu sun watsa masu zanga zanga, sun fadi dalili

Tinubu ya yi fatali da dawo da tallafi

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu a bayyana musabbabin cire tallafin man fetur a Najeriya duk da matsalolin da suka biyo baya.

Tinubu ya ce cire tallafin ya zama dole duk da halin kunci da wahala da hakan ya jefa yan Najeriya a ciki na tsawon lokaci

Shugaban ya bayyana haka ne yayin jawabinsa ga ƴan ƙasa da safiyar yau Lahadi 4 ga watan Agustan 2024 a birnin Tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.