Tinubu Ya Yi Magana Kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Mai a Jawabinsa, Bayanai Sun Fito
- Shugaba Bola Tinubu ya yi fatali da maganar dawo da tallafin mai duk da korafi da ake ta yi kan haka a fadin ƙasar
- Tinubu ya ce daukar wannan mataki ya zama dole duk da halin kunci da hakan ya jefa al'ummar Najeriya baki daya
- Shugaban ya kuma bukaci matasa masu zanga-zanga da su dakatar da kudurinsu wurin zuwa teburin tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya.
Tinubu ya yi fatali da dawo da tallafin kamar yadda ake ta kira musamman yayin zanga-zangar da ake yi.
Tinubu ya yi jawabi ga ƴan Najeriya
Shugaban ya bayyana haka ne yayin jawabi ga ƴan ƙasa a yau Lahadi 4 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce cire tallafin ya zama dole duba da haɓakar tattalin arziki da ya kawo Najeriya duk da wahalar da aka shiga dalilin haka.
Shugaban ya ce tsawon lokaci tattalin arzikin Najeriya yana cigaba da samun koma bayan kafin ya dauki wasu matakai, Daily Trust ta tattaro.
Tinubu ya fadi wahala da Najeriya ta shiga
"Shekaru da dama tattalin arzikin Najeriya na samun koma baya saboda wasu matsaloli dangane da matakai da ake dauka a kasar."
"Hakan ya jawo ba mu iya amfani da wasu matakai na gaggawa domin dakile manyan matsalolinmu a Najeriya."
"Wannan ya saka ni daukar matakin cire tallafin mai da ya jawo wahalhalu amma kuma ya zama wajibi domin bunkasa tattalin arzikinmu."
- Bola Tinubu
Wannan na zuwa ne yayin da ake sa ran shugaban zai kwantar da hankulan al'ummar kasar wurin ɗaukar wasu matakai domin dakile zanga-zanga da ake yi.
Tinubu ya yi magana kan zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar kan halin kunci da yunwa.
Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da su gaggauta dakatar da zanga-zangar su fito domin a tattauna.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin jawabinsa ga ƴan Najeriya a yau Lahadi 4 ga watan Agustan 2024 a birnin Abuja yayin da ke cigaba da zanga-zanga.
Asali: Legit.ng