Ana Tsaka da Zanga Zanga a Najeriya, Gobara Ta Kama a Kamfanin NNPCL
- Wasu daga cikin rijiyoyin kamfanin mai na NNPCL sun ci karo da matsala yayin da wata gobara ta kama a Rivers
- Hukumar kula da albarkatun mai ta NUPRC ita ta tabbatar da faruwar lamarin a daren ranar Juma'a 2 ga watan Agustan 2024
- Hukumar ta ce an yi nasarar dakile matsalar da taso yaɗuwa tare da kokarin neman kwashe man da ke rijiyoyin nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - An shiga fargaba bayan wuta ta kama wani bangare na kamfanin mai na NNPCL a jihar Rivers.
Hukumar kula da albarkatun mai ta NUPRC ta tabbatar da faruwar lamarin a rijiyar mai ta Akaso 4 Wellhead da NNPCL ke kula da ita.
Gobara ta kama a rijiyar man NNPCL
Wannan na kunshe ne a cikin kwanta sanarwa da kakakin hukumar, Laide Shonola ta fitar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shonola ta ce gobarar ta yadu har zuwa bakin kogi a ranar 2 ga watan Agustan 2024 da misalin karfe 11:12 na dare.
Ta ce an yi gaggawa tura jami'an kashe gobara inda suka yi nasarar dakile matsalar nan take, ThisDay ta tattaro.
An yi nasarar lashe gobarar rijiyar mai
"NNPCL ta dauki matakin tura jami'ai wurin da lamarin ya faru inda suka kange wurin da gobarar ta kama domin kiyaye faruwar hakan a gaba."
"Suna kokarin kwashe man da ke wurin inda aka kira kwale-kwale daga sojojin ruwa domin aiwatar da hakan."
- Laide Shonola
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu ainihin musabbabin faruwar iftila'in ba.
Shugaban NNPCL, Kyari ya kalubalanci Dangote
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kamfanin Mele Kyari ya yi martani kan zargin ma'aikatan kamfanin suna da rijiyoyin mai a kasar Malta.
Kyari ya musanta kazafin inda ya ce bai taba sanin wannan maganar ba kuma idan akwai za su yi bincike mai zurfi a kai.
Hakan ya biyo bayan takun-saka tsakanin sabon matatar man Dangote da wasu masu ruwa da tsaki a kamfanin NNPCL.
Asali: Legit.ng