Kwana 1 da Sace Shi, Shugaban Karamar Hukuma Ya Kubuta Daga 'Yan Bindiga Bayanai Sun Fito
- Kwana daya bayan sace shugaban riko na karamar hukuma a jihar Kogi, mutumin ya yi nasarar kubuta daga 'yan bindiga
- Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da kubutar Zacchaeus Dare-Michael da wasu daga cikin hadimansa da aka sace
- Hakan na zuwa ne bayan yin garkuwa da shugaban rikon karamar hukumar Kabba/Bunu a kan hanyar Kaba zuwa Okene
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Rundunar 'yan sanda a jihar Kogi ta sanar da kubutar shugaban karamar hukumar Kabba/Bunu da aka yi garkuwa da shi.
An sace Hon. Zacchaeus Dare-Michael ne a jiya Juma'a 2 ga watan Agustan 2024 a kan hanyar Okene zuwa Kaba a jihar.
Kogi: Shugaban karamar hukuma ya kubuta
Kakakin rundunar a jihar, SP Williams Ovye-Aya shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Williams ya ce shugaban rikon na karamar hukumar ya yi nasarar kubucewa da safiyar yau Asabar 3 ga watan Agustan 2024.
Ya ce Dare-Michael ya samu nasarar kubuta ne da wasu daga cikin hadimansa da aka sace su tare a jiya Juma'a a jihar, cewar Punch.
Kogi: 'Yan sanda sun tabbatar da lamarin
"Ina mai tabbatar muku da cewa shugaban karamar hukumar ya samu nasarar kubucewa da safiyar yau Asabar."
"Jami'anmu da ke yankin Kabba sun tabbatar mana da haka, wannan na daga cikin ikon Allah a ce shugaban ya kubuta."
"Mun godewa Allah wanda ya ba shugaban damar kubucewa da kuma komawa ga iyalansa cikin koshin lafiya."
- Williams Ovye-Aya
Rundunar 'yan sanda ta ce ta baza jami'anta domin cigaba da farautar sauran wadanda ke hannun 'yan bindiga.
Yadda aka sace shugaban karamar hukuma
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Kabba/Bunu na rikon kwarya a jihar Kogi.
An sace Zacchaeus Dare Michael ne bayan maharan sun yi awon gaba da kantoman tare da wasu daga cikin hadimansa zuwa wurin da ba a sani ba.
Lamarin ya faru ne a jia Juma'a 2 ga watan Agustan 2024 a kan hanyar Kaba zuwa Okene da ke jihar a Arewata ta Tsakiyar Najeriya.
Asali: Legit.ng