"Abin da Muke Gargadi Tun Tuni Ya Faru”: Malamin Musulunci Ya Soki Shugabanni
- Yayin da ake cigaba da zanga-zanga a Najeriya, Malamin Musulunci ya koka kan yadda suka gargadi gwamnati tuntuni
- Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya ce gwamnatin ba ta shirya daukar mataki ba tun kafin abin ya faru
- Malamin ya kuma shawarci mutane da suke fita neman 'yanci amma suke barna da su ji tsoron Allah kan lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Fitaccen malamain Musulunci, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya yi magana kan zanga-zanga
Malamin ya ce tuntuni suke gargadin gwamnati ka da a zo lokacin da za a kai mutane bango amma ba su dauki mataki ba.
Zanga-zanga: Dokoro ya soki gwamnati
Sheikh Dokoro ya bayyana haka ne a cikin wani karatunsa da ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin malamin ya ce malmai sun ba da gudunmawa da yawa wurin dakile matsaloli amma gwamnatin ba su gani bare su gode musu.
"Maganar zalunci, an zalunci talakawan kasa babu wanda ba shi da masaniya, kowa ya yadda da haka."
"Kuma mutanen nan suna da hanyar sassauta abubuwa amma ba su saurari abin da muke fada ba."
"Tuntuni muke ta cewa su saurara kada a zo lokacin da za a kai mutane bango tun ba a fara tunanin zanga-zanga ba muke magana."
"Tun kafin Ramadan muke magana a kai, kada ku bari a kai mutane bango amma suka yi watsi da mu."
- Sheikh Adamu Dokoro
Sheikh Dokoro ya gargadi masu zanga-zanga
Sheikh Dokoro ya ce kwata-kwata gwamnatoci ba su san amfanin malamai da abin da suka tare musu ba.
Malamin ya gargadi masu barna a zanga-zanga da su sani Allah zai tambaye su duk barnar da suka aikata.
Dokoro ya soki malamai bayan ziyartar Tinubu
Kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Adamu Muhammad Dokoro ya caccaki malamai bayan ziyartar Bola Tinubu.
Malamin ya ce ba bukatar hakuri ko wasu tsare-tsare jama'a suke bukata ba daga gare shi illa daukar matakai nan take
Sheikh Dokoro ya lissafo abubuwa guda biyar da ya kamata Shugaba Tinubu ya kaddamar domin kawo karshen matsalolin.
Asali: Legit.ng