Dalilin Shigata Zanga Zangar Lumana a Kano Inji Tsoho Mai Shekaru Kusan 70 a Duniya
- Bashir Alhassan da aka fi sani da Ya Sayyadi wani bawan Allah ne da aka ga hotunansa su na yawo a filin zanga-zangar lumana
- Wannan tsoho mai shekaru fiye da 60 a duniya ya fito gaban kowa a makon jiya, ya na kuka da kuncin rayuwa a Najeriya
- Tun da Bashir Alhassan yake, ya fadawa Legit bai taba ganin talaka ya shiga halin kuncin rayuwa da wayyo Allah irin yau ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Bashir Alhassan haifaffen garin Kano ne wanda ya ga ji kuma ya ga yau, amma ya ce bai taba ganin kunci irin na yanzu ba.
Dattijon da aka Haifa a garin Diso a karamar hukumar Gwale a jihar Kano, ya koka game da yadda aka shiga matsancin hali a Najeriya.
Hirar Legit Hausa da dattijo mai zanga-zanga
A zantawarsa da Legit a ranar Juma’a, Malam Bashir Alhassan mai shekara 66 a duniya ya fada mana dalilinsa na shiga zanga-zanga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa kuncin rayuwar ta yi yawa, an jefa mutane a masifa da yawa a zamanin nan tamkar kamar babu gwamnati mai-ci a kasa.
Yunwa ta jawo tsoho shiga zanga-zanga
Malam Bashir Alhassan ya ce mutane su na mutuwa saboda yunwa da mugun tsadar abinci a maimakon gwamnati ta taimakawa talaka.
Tsohon ya buga misali da masallacinsu a unguwar Dorayi, inda ya ce kusan duk sallah sai an ji mata sun zo barar abin da za a ci a gidajensu.
"Allah bai yi gwamnati saboda irin haka ba. Abin takaicin kudi ya fi mutum muhimmanci a wurin masu mulki."
"Ya kamata masu mulki su shiga taitayinsu, tara kudin nan ba alheri ba ne, azabar lahira ake ji masu tsoro."
- Bashir Alhassan
A zantawarmu da shi, tsohon ya koka kan yadda masu mulki ke karbar albashin miliyoyi, amma su na kyashin kara albashin ma’aikata.
Gara mulkin soja da farar hula?
Tun kafin Najeriya ta samu ‘yanci aka haifi wannan bawan Allah, amma ya ce mulkin soja ya fi alheri a kan tsarin farar hulan kasar nan.
"Duk duniya babu inda ake yin irin wannan sai Najeriya. Mutanen nan zabensu aka yi. Da akwai tsoron Allah da ba haka ba."
“Gara mulkin soja sau miliyan Wallahi. Da sojoji za su karba mulkin da ya fi Wallahi. Saboda da sojoji za su karba, na fi kowa murna.”
“Ba mu zabe su saboda su jefa mu a yunwa da bala’i da wahala ba.”
- Bashir Alhassan
Mai zanga-zanga ya koka da shugabanni
A cewarsa, gwamnatocin jihohi da tarayya ba su tausayin talaka, ya koka kan yadda aka murkushe kananan hukumomi a kasar nan.
Da kananan hukumomi za su kafu da kyau da an fi samun sauki, yake cewa da kamar wahala mutumin kauye ya iya ganin gwamnan jiha.
An yi huduba bayan barkewar zanga-zanga
A wani rahoto, an ji cewa limamin Juma'a, Farfesa Ahmad Bello Dogarawa ya yi kira ga duka shugabannin da ke mulki a hudubar da ya yi.
Ahmad Bello Dogarawa ya ce ko shakka babu, wajibi ne shugabanni su tuna cewa Allah madaukin Sarki zai tambaye su a ranar kiyama.
Asali: Legit.ng