Karin Albashi: Fargabar Zanga Zanga Ta Tilasta wa Gwamna a Arewa Kafa Kwamiti

Karin Albashi: Fargabar Zanga Zanga Ta Tilasta wa Gwamna a Arewa Kafa Kwamiti

  • Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazak ya kafa kwamitin mutane 21 saboda mafi karancin albashin ma'aikata
  • Gwamna AbdulRazak ya dauki wannan matakin ne domin inganta rayuwar ma'aikata yayin da ake tsaka da zanga-zanga
  • Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar a wannan mako da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Yayin da ake cigaba da zanga-zanga, gwamnatin jihar Kwara ta kafa kwamitin duba kan mafi karancin albashi.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya kafa kwamiti mai mutane 21 domin tabbatar da mafi karancin albashin a jihar.

Gwamna ya kafa kwamitin game da mafi karancin albashi
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara ya kafa kwamiti kan sabon albashin N70,000. Hoto: AbdulRahman AbdulRazak.
Asali: Facebook

Kwara: Gwamna ya kafa kwamitin karin albashi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye ya fitar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan gwamna a Arewa ya ki albashin N70,000, NLC ta fadi matakin da za ta dauka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ajakaya ya ce gwamnan ya dauki matakin ne saboda amincewa da karin albashin N70,000 ga ma'aikata a Najeriya.

Ya ce mambobin kwamitin sun hada da wakilai daga gwamnatin jihar da kungiyar kwadago da kuma kamfanoni masu zaman kansu, cewar Leadership.

Kwara: Mambobin da ke cikin kwamitin albashin

"Kwamitin wanda shugaban ma'aikatan jihar zai jagoranta akwai kwamishinan kudi da daraktan fansho a matsayin sakatare."
"Sauran mambobin sun hada da kwamishinan kudi da na ayyuka da sufuri da kuma na sadarwa da harkokin sarakunan gargajiya.
"A bangaren kungiyar kwadago akwai shugabanta da shugaban TUC da sauran kungiyoyin kwadago da na gwagwarmaya."

- Rafiu Ajakaye

Ajakaye ya ce wannan mataki zai ba kwamitin damar duba kan mafi karancin albashin domin daukar mataki na gaba kan haka.

NLC ta gargadi gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya

Kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC a jihar Gombe ta dauki zafi kan kalaman gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya gwangwaje Buba Galadima da mukami, ya yi wasu nade nade

Kungiyar ta ce za ta yi dukka mai yiwuwa domin tabbatar da ma'aikata sun ci moriyar sabon albashin N70,000 da aka tabbatar.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Inuwa ya ce ba zai iya biyan sabon albashin ba saboda rashin kudi da ake fama da shi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.