Ana Tsaka da Zanga Zanga, Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugaban Ƙaramar Hukuma a Arewa
- Ƴan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Kabba/Bunu a jihar Kogi, Barista Zacchaeus Dare Michael tare da wasu hadimai
- Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindiga sun tare kantoman a kan titin Kabba zuwa Okene, sannan suka tafi da shi zuwa cikin daji
- Wani mai suna Olayinka Samuel ya ce a halin yanzu hukumomi na bukatar sahihan bayanan sirri da za su taimaka masu wajen ceto su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Kabba/Bunu na rikon kwarya a jihar Kogi, Zacchaeus Dare Michael.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da kantoman tare da wasu daga cikin hadimansa zuwa wurin da ba a sani ba.
Wani mai suna, Olayinka Samuel, ya bayyana cewa an yi garkuwa da Barista Dare ne tare da wasu mukarrabansa a titin Kabba-Okene a jihar Kogi, cwwar rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka sace kantoma a Kogi
"Rahotannin da muka samu sun nuna cewa an yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Kabba/Bunu na rikon kwarya (CTC), Barista Zacchaeus Dare Michael tare da wasu muƙarrabansa.
"Wasu ƴan bindiga da ba sa san ko su waye ba sun yi awon gaba da kantoman a kan titin Kabba zuwa Okene a yankin Kebba. Hukumomi suna neman duk wani sahihin bayani da zai taimaka wajen ceto su.
"Ina kira ga ɗaukacin al'umma da su tama mu da addu'ar Allah ya kuɓutar da su cikin gaggawa, tare da neman taimakon Allah da kariya a cikin wannan mawuyacin lokaci.”
- Olayinka Samuel.
Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko gwamnatin jihar Kogi kan wannan lamarin.
Bom ya halaka mutane a Borno
Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa wani bom da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram suka dasa ya tarwatse a wurin mai shayi.
Akalla mutane 19 suka mutu sakamakon tashin bom ɗin a kauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno ranar Laraba, 31 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng