Sanata Mai Ci Na Daukar Nauyin Masu Zanga Zanga? Gaskiya Ta Fito
- Yayin da ake zargin sanata mai ci da daukar nauyin masu zanga-zanga, Sanata Ireti Kingibe ta yi martani kan lamarin
- Sanata Kingibe ta musanta karairayin da ake yi inda ta ce tsohon bidiyo aka dauko domin bata musu suna yayin zanga-zanga
- Hakan ya biyo bayan zargin da ake yadawa cewa an gano sanatan tana raba abinci ga masu zanga-zanga a birnin Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sanata Ireti Kingibe ta yi martani kan zargin da ake yi mata na daukar nauyin masu zanga-zanga a birnin Abuja.
Kingibe ta musanta cewa tana da hannu a lamarin wanda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi zargi yayin da ake zanga-zanga.
Zanga-zanga: Sanata ta nuna damuwa kan zarginta
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin hadiminta a bangaren sadarwa, Kennedy Mbele, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatar ta ce ta ji ba dadi kan wadannan karairayi da aka danganta da ita yayin da ake cigaba da zanga-zanga a kasar.
Ta ce bidiyon da ake yadawa ya kai makwanni shida inda ake wata ganawa na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar LP.
Sanata ta fadi gaskiya kan masu zanga-zanga
"Na kadu da samun labarin karairayi cewa ni nake daukar nauyin masu zanga-zanga musamman a birnin Abuja."
"Faifan bidiyon da ake yadawa ya kai makwanni shida yayin wata ganawa da shugabannin jam'iyyar LP inda NLC ke zanga-zanga."
"A matsayin manyan jam'iyyar, da ni da sanatoci da sauran Mambobin Majalisar Wakilai da Peter Obi mun fita domin kwantar musu da hankali."
- Ireti Kingibe
Sanata Kingibe ta ce a yanzu masu kitsa karairayin sun dawo da tsohon bidiyo domin nuna cewa ita da Peter Obi suna daukar nauyin zanga-zanga.
Wike ya zargi Sanata kan zanga-zanga
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa an gano wata sanata da ke daukar nauyin masu yin zanga-zanga.
Wike ya bayyana haka yayin taro da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro inda ya ce an gano sanata na ba da abinci ga masu zanga-zanga.
Asali: Legit.ng