"Babu Ruwanmu," Gwamnati Ta Kare Kanta Bayan Tangardar Intanet da Rufe Layukan Waya

"Babu Ruwanmu," Gwamnati Ta Kare Kanta Bayan Tangardar Intanet da Rufe Layukan Waya

  • Gwamnatin tarayya ta musanta zargin da ake na cewa ita ta bayar da umarnin rufe layuka da kawo tangarda a sadarwar kasa
  • Kwanaki gabanin gudanar da zanga-zanga a kasar nan da ma lokacin da aka fara ta, an rufe layukan al'ummar ƙasar nan
  • Amma daga baya, hukumar kula da harkokin sadarwa ta ƙasa (NCC) ta bayar da umarnin a gaggauta bude layukan jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta musanta cewa ta na da hannu cikin matsalolin sadarwa da ake fuskanta a kasar nan.

Layukan wayoyin mazauna Najeriya ya fuskanci matsala, inda aka rufe wadansu layukan, wasu kuma su ka daina aiki kwata-kwata,yayin da wasu ke zargin saboda zanga-zanga ne.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Kiristoci sun ba Musulmai masu sallar Juma'a kariya ana tsaka da zanga zanga

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Gwamnati ta musanta umarnin rufe layukan waya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa da yawa an yi zargin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ce ta umarci a yi hakan a kokarin dakile zanga-zangar adawa da manufofinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba mu san da rufe layuka ba," Gwamnati

Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani ya ce ofishinsa bai bayar da umarnin kawo tangarda a layuka ba.

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Ministan na ganin yawan jama'ar da ke aiki da kafar yanar gizo ma kadai ya isa haddasa matsala, duk da ba lallai wannan ne dalili ba.

Mista Tijani ya kara da cewa duk da matsalolin da galibin'yan kasa ke fuskanta, har yanzu akwai masu morar intanet.

Gwamnati na neman karin karfin intanet

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai shiri na musamman domin bunkasa karfin intanet a kasar nan.

Kara karanta wannan

Jama'a sun yi kunnen ƙashi, an fito zanga zanga a rana ta 2 duk da dokar hana fita

Ministan sadarwa, Bosun Tijani ya ce duk da majalisar zartarwar tarayya ta amince da hakan, ba za a kammala aikin cikin watanni shida ba.

An samu tangardar intanet a Najeriya

A baya mun ruwaito cewa mazauna jihar Kano sun koka a kan matsanancin rashin ingantaccen intanet da kuma targada a kokarinsu na kiran waya.

'Yan kasuwa na daga cikin wadanda lamarin ya fi yi wa rashin dadi a sa'ilin da wasu ke zargin ko shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga ne ya sa aka samu matsala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.