Jama'a Sun Yi Kunnen Ƙashi, An Fito Zanga Zanga a Rana ta 2 Duk da Dokar Hana Fita

Jama'a Sun Yi Kunnen Ƙashi, An Fito Zanga Zanga a Rana ta 2 Duk da Dokar Hana Fita

  • Wasu daga cikin jama'ar jihar Jigawa sun yi biris da umarnin gwamnati na dokar hana fita inda wasu su ka bazama titunan jihar
  • Daga cikin wadanda su ka fita zanga-zangar a yau sun yi kicibis da jami'an tsaro yankin zai yayin da aka hana su wucewa
  • A zantawarsa da Legit, kakakin rundunar jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyana cewa har yanzu akwai dokar hana zirga-zirga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Jama'a a Jigawa sun fito zanga-zanga duk da haramcin fita na awanni 24 da gwamnatin jihar ta sanya.

Jamai'an tsaro sun hana mutanen shiga yankin Zai inda ake da shaguna da sauran kadarorin gwamnati domin gujewa tashin hankali.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan sanda na kokarin kakkabe miyagu, an kama 'yan daba 50 a Katsina

Jigawa
Jama'a sun fito zanga-zanga duk da dokar hana fita Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa wasu mutanen Shuwarin da ke Dutse sun fito, yayin da aka shiga rana ta biyu da zanga-zangar adawa da manufofin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce masu zanga-zanga na kokarin kutsawa babban birnin jihar, amma jami'an tsaro sun tabbatar da dokar hana fita, tare da kama wasu cikinsu har da kananan yara.

Zanga-zanga: An samu zaman lafiya a Jigawa

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa duk da an sassauta dokar hana zirga-zirga zuwa karfe 2.30pm, yanzu dokar hana fitar ta ci gaba.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam ne ya bayyanawa Legit hakan ta wayar tarho.

Ya ce yanzu haka jihar Jigawa lafiya kalau, domin an fara samun zaman lafiya kamar yadda ake mora gabanin zanga-zangar.

An kama masu satar kaya a zanga-zanga

Kara karanta wannan

An shiga rana ta 2 na zanga zanga, jama'a sun fara hallara a garin Tinubu

A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta cafke matasa maza da mata da ake zargi da hannu wajen daka wasoso a kan kayan jama'a lokacin gudanar da zanga-zanga.

Yayin fara zanga-zangar lumana a Kano, an samu wasu bata-gari da sauran mutanen gari, ciki har da mata su na kwashe kayan jama'a da wasu kayan abinci a sassan jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.