Dokar Hana Fita: Abba Ya Dauki Mataki 1 Domin Ba Kanawa Damar Zuwa Sallar Juma’a

Dokar Hana Fita: Abba Ya Dauki Mataki 1 Domin Ba Kanawa Damar Zuwa Sallar Juma’a

  • Abba Kabir Yusuf ya sassauta dokar hana fita ta awanni 24 da ya sanya a fadin jihar a jiya Alhamis bayan rigimar da ta balle
  • Mai tallafawa gwamnan kan kafofin sada zumunta, Abdullahi I. Ibrahim ya fitar da sanarwar sassauta dokar a yau Juma'a
  • Abdullahi ya ce an sassauta dokar ne na tsawon awanni biyar domin baiwa al'ummar Musulmi damar zuwa sallar Juma'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamnatin Kano ta sake waiwayar dokar zaman gida ta awanni 24 da ta sanya a fadin jihar a jiya Alhamis, 1 ga watan Agusta.

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya sanya dokar hana fita ne biyo bayan tashin hankulan da aka samu saboda zanga-zangar da ake yi.

Kara karanta wannan

Bayan gwamna a Arewa ya ki albashin N70,000, NLC ta fadi matakin da za ta dauka

Gwamnatin Kano ta yi magana kan sassauta dokar hana fita
Gwamnatin Kano ta sassauta dokar hana fita saboda aje masallacin Juma'a. Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Sai dai babban mai tallafawa gwamnan ta fuskar kafofin sada zumunta, Abdullahi I. Ibrahim ya fitar da sanarwa a shafinsa na X inda ya ce an sassauta dokar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: An sassauta dokar hana fita

Abdullahi Ibrahim wanda ya fitar da sanarwar a yau Juma'a ya ce Gwamna Yusuf ya sassauta dokar ne domin ba al'umma damar zuwa sallar Juma'a.

Mai tallafawa gwamnan ya ce an sassauta dokar ne na wanni biyar kacal, daga karfe 12 na rana zuwa karfe 5 na yamma.

Ya kuma ce dokar zaman gidan za ta ci gaba da zarar wannan wa'adin sassaucin da aka deba ya kare.

A cewar sanarwar da Abdullahi ya fitar:

"Gwamnatin Kano ta amince a je masallaci daga 12:00 na rana zuwa 5:00 na yamma, inda daga wannan lokaci ne dokar zaman gidan za ta ci gaba."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Bayan ƙaƙaba dokar kulle, gwamna ya tsara yadda za a yi Sallar Jumu'a

Duba sanarwar a kasa:

An gano dalilin tashin hankali a Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnan Kano ya dora alhakin rikidewar zanga-zanga zuwa tashin hankali a Kano a kan wasu marasa kishin jihar.

Abba Kabir Yusuf ya ce an dauko hayar wasu bata-gari mota-mota zuwa jihar Kano a safiyar yau, inda su kuma su ka fara tayar da hatsaniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.