PDP Ta Cire Adawa Ta Fadawa Tinubu Hanyar Shawo Kan Masu Zanga Zanga

PDP Ta Cire Adawa Ta Fadawa Tinubu Hanyar Shawo Kan Masu Zanga Zanga

  • Jami'yyar adawa ta PDP ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan zanga zangar da ta barke
  • PDP ta ambaci abubuwan da ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi domin kwantar da hankalin matasan Najeriya
  • Sakataren yada labaran PDP na kasa, Hon. Debo Olagunagba ne ya yi kiran ga gwamnatin tarayya domin kawo zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu kan shawo kan matasa masu zanga zanga.

PDP ta fadi abubuwan da ta fadawa gwamnatin APC a baya amma ta ki dauka wanda a cewarta hakan ne ya haifar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Jagororin addini sun cire tsoro sun tunkari Tinubu da bukatun talakawa

Jam'iyyar PDP
PDP ta shawarci Bola Tinubu kan zanga zanga. Hoto: People's Democratic Party - PDP
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sakataren yada labaran jam'iyar PDP na kasa, Hon. Debo Olagunagba ne ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga zanga: Shawarar jam'iyyar PDP ga Tinubu

Jami'yyar PDP ta yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan janye tsare tsare da ya kawo da ta ce suna jefa mutane cikin wahala.

PDP ta kuma bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya yi jawabi na musamman ga yan kasa kan halin da al'umma ke ciki na zanga zanga da wahalar rayuwa.

A cewar PDP, daukan matakan da ta fada za su sa a samu kwanciyar hankali da kawo saukin rayuwa a Najeriya.

Rashin karbar shawara: PDP ta zargi APC

This Day ta wallafa cewa PDP ta zargi APC da rashin karbar shawarwari masu amfani da ta ba ta a lokuta mabanbanta da suka gabata.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Tinubu sun yi kishiyar zanga zanga a Kano, su na goyon bayan gwamnati

Sakataren yada labaran PDP, Debo Olagunagba ya ce sun ba gwamnatin APC shawarwari a kan tattalin arziki amma ta ki sauraro.

A cewar Debo Olagunagba rashin karɓar shawarwari ne yasa kasa ta rikice saboda haka suke fata APC za ta sauraresu a wannan karon.

Wike ya nemi sulhu bayan fara zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi magana a karon farko bayan matasan Najeriya sun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a jihohi.

Ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ne ya yi kira ga matasan Najeriya domin neman hanyar kawo karshen zanga zangar baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng