An Shiga Rana ta 2 na Zanga Zanga, Jama'a Sun Fara Hallara a Garin Tinubu
- Yau ce rana ta biyu da fara zanga-zangar kwanaki 10 domin adawa da manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- 'Yan Najeriya na ganin manufofin gwamnatin tarayya ne su ka kara jefa su a cikin matsin rayuwa da kuncin talauci
- An samu tashe-tashen hankula a wasu jihohin Arewacin kasar, amma an fara hallara a Legas domin shiga rana ta biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Legas - Duk da yadda aka samu tashe-tashen hankula a jihohin kasar nan saboda zanga-zanga, jama'a sun fara taruwa a Legas domin fara tattaki.
Ranar Alhamis aka fara zanga-zangar kwanaki 10 wacce ake sa ran za ta nunuwa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu cewa ana jin jiki a kasar nan.
Jaridar The Nation ta tattara cewa yanzu haka masu zanga-zanga sun shirya ci gaba da tattakinsu, an fara taruwa a Gani Fawehinmi Freedom Park, Ojota, Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran idan an kammala taruwa, za a ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana domin neman sauƙin matsin rayuwa da ake ciki.
An tsaurara tsaro gabanin zanga-zanga
An hango dandazon jami'an tsaro jibge tare da jama'a a kwana na biyu da fara gudanar da zanga-zanga.
An ji jami'an tsaron su na kokarin nusar da jama'a cewa kar su rufe hanyoyi su tayar da hatsaniya yayin zanga-zangar rashin jin dadin manufofin gwamnatin tarayya.
Jami'an tsaro sun tabbatar da cewa za su ci gaba da bayar da tsaro ga dukkanin masu fita zanga-zanga matukar sun bi doka.
Zanga-zanga: Gwamnati ta sanya dokar hana fita
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar hana fice da shige a fadin jihar na tsawon awanni 24 saboda yadda aka samu matsala yayin zanga-zanga.
Tun da fari, gwamna Abba Kabir Yusuf ya zargi wasu bata-gari da dauko hayar 'yan daba da su hargitsa garin na maimakon gudanar da zanga-zangar lumana da ake shirya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng