Gwamna Ya Sanya Dokar Zaman Gida Ta Awanni 24, Ya Tsara Yadda Za a Yi Sallar Jumu'a

Gwamna Ya Sanya Dokar Zaman Gida Ta Awanni 24, Ya Tsara Yadda Za a Yi Sallar Jumu'a

  • Gwamna Umar Namadi ya sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a Jigawa bayan tashe tashen hankula a lokacin zanga-zanga
  • Ɗanmodi ya bayyana cewa za a sassauta dokar daga karfe 12:00 zuwa 2:30 na rana domin ba mutane damar zuwa Masallacin Jumu'a
  • Wannan mataki na zuwa ne a ranar farko da fara zanga-zangar yunwa wanda ta canza salo zuwa ƙone-ƙone da satar dukiyar al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonɓshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya dokar zaman gida ta tsawon sa'o'i 24 yayin da zanga-zangar lumana ta riƙide ta zama tashin hankali.

Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya sanar da ƙaƙaba dokar a wani jawabi na kai tsaye da ya yi ranar Alhamis da daddare.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita? Uba Sani ya magantu ana zanga zanga

Gwamna Umar Namadi.
Gwamna Umar Namadi Ɗanmodi ya snaya dokar kulle a faɗin jihar Jigawa Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

Zanga-zanga ta koma tashin hankali

A ranar farko ta zanga zangar yunwa wadda masu shiryawa suka ce ta lumana ce, an yi kashe-kashe, kone-kone da satar dukiya a jihohi da dama ciki hada Jigawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Domin daƙile yaɗuwar ɓarnar da aka yi, Gwamna Umar Namadi ya sanya dokar kulle a faɗin kananan hukumomin jihar, kamar yadda Leadership ta kawo.

Gwamnan ya bayyana halin da ake ciki a jihar a matsayin abin takaici matuka kuma ba zai zama mafita ga bukatun mutane ba.

Gwamna ya tsara yadda za a yi Sallar Jumu'a

"Ba za mu lamunci wannan yanayi da zanga-zangar lumana ta rikiɗe ta zama tashe tashen hankula da satar dukiya da sunan ganima ba, kwata kwata ba al'adar mu ba ce.
"Saboda haka ba za mu bari a ci gaba ba, muna sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa da aka sanya dokar hana fita ta awa 24 sun kai 4, an samu cikakken bayani

"Amma saboda Sallar Jumu'a, za a sassaunta dokar daga ƙarfe 12:00 zuwa ƙarfe 2:30 na rana domin bai wa mutane damar zuwa Masallaci."

Gwamna Namadi ya ƙara da cewa gwamnati da jami'an tsaro za su ci gaba da sanya ido da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al'umma a Jigawa.

Idan ba ku manta ba masu zanga-zanga sun cinnawa babbar hedkwatar APC wuta a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Zanga-zanga: Mutanen Jigawa sun koka

Aminu Maje, wani mazaumin Birnin Kudu ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa lamarin ya yi muni sosai musamman a Dutse, Haɗeija da Birnin Kudu.

Ya ce a zahirin gaskiya abin da aka yi ba zanga-zanga ba ce, ɓarna ce kawai da satar kayan gwamnati.

Aminu ya ce:

"Abin ya ta'azzara sosai a nan Birnin Kudu, Dutse da Haɗeija, masu zanga-zanga sun yi ƙone-ƙone, sun fasa kayayyakin gwamnati, sun ɗauke wasu, ga shi sun ja mana zaman gida."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Gwamna Abba ya sanya dokar hana fita a Kano, ya umarci jami'an tsaro

Ƴan sanda sun tarwatsa mutane a Bauchi

A wani rahoton, an ji ƴan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga waɗanda suka taru a kofar fadar mai martaba sarkin Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun nemi ganawa da sarkin tun da safiyar Alhamis amma ƴan sanda suka hana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262