“Jami’an Tsaro Sun Gano Sanata Mai Daukar Nauyin Zanga Zanga,” Minista Wike Ya Yi Magana
- An bankado wani sanata da ake zargin yana da hannu wajen ingiza zanga-zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu a fadin kasar
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan inda ya ce tuni jami’an tsaro suka iya tantance dan majalisar tarayyar
- Ministan ya kuma yi kira ga masu zanga-zanga a Abuja da su yi biyayya ga umarnin kotu na hana su shiga filin taron Eagles Square
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce hukumomin tsaro sun gano wani sanata da ake zargi da daukar nauyin zanga-zanga a babban birnin kasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja, a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, bayan wani taro da shugabannin hukumomin tsaro suka yi.
Legit Hausa ta ruwaito cewa an fara zanga-zangar da aka shirya a jiya Alhamis a Abuja da kuma wasu sassan kasar nan duk da kiran da jami’an gwamnati suka yi na cewa ‘yan kasar su guji zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene sanatan? Wike ya yi magana
Nyesom Wike ya ce nan gaba kadan hukumomin tsaro za su gayyaci sanatan domin ya amsa wasu tambayoyi a cewar rahoton jaridar Vanguard.
Ministan Abuja ya ce an fara bin diddigin sanatan ne lokacin da ya dauki rakiyar jami'an tsaro zuwa inda masu zanga-zangar suke tare da raba masu abinci.
“Wani sanata ne ke ba masu zanga-zangar abinci. Idan lokacin ya yi, jami’an tsaro za su gayyaci sanatan, su gano yadda zai rika daukar nauyin bore wa gwamnati mai ci.”
- Nyesom Wike.
Wike ya yi kira ga masu zanga-zanga
Channels TV ya ruwaito minista ya kuma gargadi masu zanga-zangar a babban birnin kasar da su yi biyayya ga umarnin kotu kuma su tsaya a iya filin wasa na MKO Abiola.
A cewar ministan, hukumomin tsaro sun samu rahoton sirri na mutanen da ke son yin garkuwa da zanga-zangar lumana wanda shi ya sa jami'an tsaro ke son masu mutane su tsaya a wuri guda.
An kona hedikwatar APC wajen zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa fusatattun matasa masu zanga-zanga sun kona hedikwatar jam'iyyar APC ta jihar Jigawa.
An ce lamarin ya faru a yammacin ranar Alhamis bayan da zanga-zangar lumana ta rikide zuwa tashin hankali a Dutse, babban birnin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng