Shekara 63: Gwamna Abba Yusuf ya Aika Muhimmin Sako ga Sarkin Kano, Sanusi II

Shekara 63: Gwamna Abba Yusuf ya Aika Muhimmin Sako ga Sarkin Kano, Sanusi II

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga sarki Muhammadu Sanusi II
  • Rahotanni sun bayyana cewa Sarki Sanusi II ya cika shekara 63 a duniya yayin da ya yi wata biyu da komawa karagar mulki
  • Gwamna Abba ya jinjinawa Sarki Sanusi II a kokarin da yake yi na ganin an yada kyawawan al'adu a Arewa da kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya cika shekara 63 a duniya, yayin da ya yi watanni biyu da komawa karagar sarki.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga sahun 'yan uwa, abokan arziki da kuma masoya wajen taya Sanusi II murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa da aka sanya dokar hana fita ta awa 24 sun kai 4, an samu cikakken bayani

Gwamnan Kano ya taya sarki Muhammadu Sanusi murnar zagayowar ranar haihuwarsa
Kano: Abba ya aika sakon taya murnar cikar sarkin Kano Sanusi II shekara 63 a duniya. Hoto: EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

Abba ya rubutawa Muhammadu Sanusi II wasika

A cikin wata budaddiyar wasika da Abba Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, gwamnan ya jinjinawa Sarki Sanusi II kan himmarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wasikar, Gwamna Abba ya ce:

"Ina amfani da wannan damar in mika sakon taya murna ga mai martaba sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a wannan rana da ya cika shekara 63 a duniya
"A matsayinsa na jagoran darikar Tijjaniyya Sufi na kasar nan, na gamsu da kokarin sarkin na hada kan mabiya darikar da ma al'ummar Musulmin Kano da kasa baki daya."

Gwamna ya jinjinawa Sarki Sanusi II

Gwamna Abba Yusuf ya jinjinawa Sarki Sanusi II a kokarin da yake yi na ganin an yada kyawawan al'adu a Arewa da ma kasashen waje.

"Ina jinjinawa mai martaba kan fadi tashin da yake yi na ganin an bunkasa al'adu a Arewacin Najeriya da ma kasashen da ke makwabtaka da kasarmu"

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi magana kan zanga zanga, ya fadi hassadar da ake yi wa jihar Kano

Gwamnan ya ce yana fatan Sarki Sanusi II zai ci gaba da amfani da kwarewa da baiwarsa wajen kawo ci gaba a jihar Kano da kasa baki day.

Kano: Abba ya sanya dokar hana fita

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya sanya dokar hana fita ta awanni 24 a fadin jihar Kano yayin da zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali.

Gwamna Abba Kabir ya sanar da dokar a yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 bayan barnar da aka tafka a wasu sassa na jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.