Zanga Zanga: Gwamna Abba Ya Sanya Dokar Hana Fita a Kano, Ya Umarci Jami’an Tsaro

Zanga Zanga: Gwamna Abba Ya Sanya Dokar Hana Fita a Kano, Ya Umarci Jami’an Tsaro

  • Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita har na tsawon awanni 24 domin dakile barnar da ake yi
  • Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis a gidan gwamnati
  • Gwamnan ya ce hakan shi ne mafita domin dakile cigaba da barnar da ake yi da lalata dukiyoyin al'ummar jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita a fadin jihar bayan zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da dokar a yau Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 bayan barnar da aka tafka.

Abba Kabir ya sanya dokar hana fita a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta sanya dokar hana fita na tsawon watanni 24. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Abba Kabir ya sanya dokar hana fita a Kano

Kara karanta wannan

Wani gwamnan Arewa ya sake hana zanga zanga, an sanya dokar awa 24 babu fita

Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a gidan gwamnatin jihar wanda hadiminsa, Abdullahi Ibrahim ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Kabir ya umarci jami'an tsaro da su tabbatar an bi dokar sau da kafa domin kare lafiya da dukiyoyin al'umma.

"Bayan duba na natsuwa kan halin da ake ciki mun tabbatar da sanya dokar hana fita na tsawon awanni 24 a jihar."
"Mun dauki wannan matakin ne domin kare cigaba da satar kayan jama'a da ruguza kasuwanci da kuma rasa rayuka."

- Abba Kabir Yusuf

Abba Kabir ya bukaci jami'an tsaro wurin yin aikinsu domin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Zanga-zanga: Jihohin da suka sanya doka

Bayan jihar Kano, jihohin Borno da Yobe su ma sun biyo sahun wadanda suka sanya dokar hana fita domin dakile matsalar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita? Uba Sani ya magantu ana zanga zanga

Wannan na zuwa ne bayan zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali da kuma sace-sacen dukiyoyin al'umma.

Sarki Sanusi II ya gargadi masu zanga-zanga

Mun kawo labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi magan mai kama hankali kan shirin gudanar da zanga-zanga a Najeriya.

Sanusi II ya shawarci matasa da su guji shiga lamarin zanga-zangar da aka shirya fita Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.

Wannan na zuwa ne yayin da aka shirya fita zanga-zanga a fadin kasar saboda halin kunci da ake ciki na tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.