Ta’addanci a Zanga Zanga: Gwamnan Arewa ya Sanya Dokar Hana Fita ta Awa 24 a Jiharsa
- Sakamakon yadda zanga-zangar lumana ta sauya zani zuwa tashin hankali, an sanya dokar hana fita ta awanni 24 a Yobe
- Gwamnati ta sanar da sanya dokar ne a yau Alhamis bayan ta gano 'yan daba na son lalata wasu kadarorin gwamnatin jihar
- Kamar yadda sanarwar mai ba gwamnan Yobe shawara kan lamuran tsaro ta nuna, yankuna uku ne wannan dokar ta shafa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a yankunan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar.
Gwamnatin jihar ta kafa dokar ta-bacin ne bayan da wasu ‘yan daba suka kwace zanga-zangar da ake yi a jihar da nufin lalata kadarorin gwamnati.
Yobe: 'Yan daba sun kwace zanga-zanga
Mai ba gwamnan Yobe shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdussallam (mai ritaya) ya sanar da hakan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da Birgediya Janar Dahiru Abdussallam ya fitar ta ce:
“Gwamnatin jihar Yobe ta damu matuka kan yanayin tsaro a garuruwan Potiskum, Gashua, da Nguru a wannan lokaci na zanga-zanga.
"Gwamnatin ta gano cewa akwai wasu 'yan daba da suka kwace zanga-zangar lumanar da nufin farwa kadarori da sace dukiyar gwamnati."
Gwamnatin Yobe ta sanya dokar hana fita
Mai ba gwamnan shawara ya ci gaba da cewa:
“Saboda haka, gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Potiskum, Gashua da Nguru.
Ana shawartar jama’a da su bi dokar hana fita da kuma zama a gida domin samun zaman lafiya a wadannan yankuna da ma jihar baki daya."
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta ba jami'an tsaro umarnin tabbatar da an bi wannan dokar a yankunan da abin ya shafa.
Gwamna Zulum ya sanya dokar hana fita
A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa Gwamna Babagana Zulum ya sanya dokar hana fita ta awanni 24 a fadin jihar Borno.
Wannan na zuwa ne bayan da wani bam ya tashi a jihar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 16 tare da jikkata mutane da dama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng