Zanga Zanga Ta Koma Fitina: An Kashe Mutum 1 Yayin da Aka Babbake Gidan Mai a Kano

Zanga Zanga Ta Koma Fitina: An Kashe Mutum 1 Yayin da Aka Babbake Gidan Mai a Kano

  • Rahotan da muke samu daga jihar Kano na nuni da cewa an kashe wani matashi mai suna Ismael Ahmad Musa a yankin Hotoro
  • Hakazalika, an ce harsashin bindiga ya samu wani matashi wanda aka garzaya da shi asibitin Aminu Kano domin ceto rayuwarsa
  • Kamar yadda rahotanni suka bayyana, masu zanga-zanga sun banka wuta a ofishin hukumar NCC, gidan mai da kuma shagon Rufaida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wani mai suna Ismael Ahmad Musa a yankin Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

An ce wanda aka kashen mazaunin Hoto Danmarke ne, kuma dan uwansa Mubarak ne ya tabbatar da mutuwarsa a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun ci karfin jami'an tsaro, an toshe babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna

An kashe mutum daya, daya kuma na kwance a asibiti a jihar Kano
Kano: An kashe matashi yayin da aka kona gidan mai da ofishin NCC. Hoto: @Princemoye1
Asali: Facebook

An kashe matashi a zanga-zanga

Jaridar Daily Trust ta ce har yanzu ba a gano ko Ismael na daga cikin matasan da ke zanga-zangar yuwa ko kawai dan ba ruwana ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni dai aka ce an yi wa mamacin sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Baya ga Ismael an ce akwai kuma wani matashi da ya samu mummunan rauni wanda aka garzaya da shi asibitin Aminu Kano (AKTH) domin ceto rayuwarsa.

Kano: An kona ginin hukumar NCC

Ana zargin cewa harsashin bindiga ne ya same shi.

A hannu daya kuma, kamfanin dillancin labaran NAN ya ruwaito cewa an cinnawa ofishin hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) na Kano wuta.

NAN ta ce wasu gungun matasa ne wadanda ke dauke da makamai suka cinnawa ofishin wuta inda kuma suka mamaye manyan titunan Kano.

Kara karanta wannan

Kano: ’Yan sanda sun tashi tsaye, matasa sun farmaki shaguna daga fara zanga zanga

An cinnawa gidan mai wuta a Kano

An ce mako mai zuwa ne aka shirya kaddamar da sabon ofishin kafin wannan ta'

A yankin Hotoro da ke Kano, rahotanni sun ce an rufe shaguna yayin da aka bankawa wani gidan mai da kuma shagon Rufaida wuta, inji rahoton Premium Times.

Wasu mazauna yankin sun yi kira ga jami'an tsaro da su gaggauta daukar matakai domin dawo da zaman lafiya da kuma kare dukiyoyin al'ummar jihar.

Zanga-zanga: An run rufe hanyar Abuja-Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa daruruwan masu zanga-zanga sun rufe babbar hanyar da ke kai mutum jihar Kaduna daga birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa saboda yawan matasan, 'yan sandan da ke wajen sun gagara yin komai kan wannan cunkuson ababen hawa da toshe hanyar ya haifar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.