Zanga Zanga ta Gamu da Cikas a Borno, Gwamna ya Sanya Dokar Hana Fita Ta Awanni 24

Zanga Zanga ta Gamu da Cikas a Borno, Gwamna ya Sanya Dokar Hana Fita Ta Awanni 24

  • Gwamna Babagana Zulum ya amince da sanya dokar hana fita ta awanni 24 a fadin jihar Borno daga yau Alhamis 1 ga watan Agusta
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso ya sanar da hakan a sanarwar da ya fitar
  • ASP Nahum Kenneth Daso ya shaida cewa an dauki matakin sanya dokar ne biyo bayan fashewar bam a kasuwar Konduga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Gwamnatin Borno ta sanar da sanya dokar hana fita ta awannni 24 a fadin jihar kuma dokar za ta fara aiki ne nan take.

Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani ga wani mummunan bam da aka dasa a kasuwar Kawori da ke yankin Konduga a jihar Borno a daren Laraba.

Kara karanta wannan

Wani bom ya tarwatse a teburin mai shayi, mutane kusan 20 sun mutu a Arewa

Gwamnatin jihar Borno ta sanya dokar hana fita ta awanni 24
Sakamakon tashim bam, gwamnati ta sanya dokar hana fita a jihar Borno. Hoto: @ProfZulum
Asali: UGC

An sanya dokar hana fita a Borno

Jaridar Punch ta ce akalla mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a fashewar bam din da ake zargin wani dan kunar bakin wake na Boko Haram ne ya tayar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a shafinsa na X.

Sanarwar mai taken, “Kakaba dokar hana fita,” ta yi nuni da cewa fashewar bam ne ya sa Gwamna Babagana Zulum ya tuntubi manyan jami’an tsaro kafin aiwatar da wannan matakin.

Maufar gwamnati na sanya dokar hana fita

Sanarwar ta ce dokar hana fitar da aka sanya a jihar na da nufin maido da doka da oda da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tono wani 'bom' da aka dasa kwana 1 gabanin fara zanga zanga

Sanarwar ta ce:

"Kuna sane da abin da ya faru a garin Kawori inda bam ya tashi tare da halaka mutane 16 da jikka mutane da dama wadanda suke kwance a asibitoci daban daban.
"Mai girma Gwamna Babagana Umar Zulum ya tuntubi shugabannin tsaro a jihar, inda ya ga ya dace a ayyana dokar hana fita na sa’o’i 24 a jihar nan take."

Kakakin rundunar 'yan sandan ya bukaci mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu kuma su bi dokar hana fita da aka sanya.

Bam ya fashe a kasuwar Borno

Tun da fari, mun ruwaito cewa wani bam da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram suka dasa ya tarwatse a wurin mai shayi da ke kasuwar Kawori a Borno.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne kwanaki uku bayan da wasu mahara suka kai hari ofishin ‘yan sanda a garin Jakana duk a karamar hukumar Konduga.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.