Malamin Addini Ya Jagoranci Matasa Zuwa Zanga Zanga a Arewacin Najeriya

Malamin Addini Ya Jagoranci Matasa Zuwa Zanga Zanga a Arewacin Najeriya

  • A yau ne al'ummar Najeriya suka fito kan tituna a faɗin ƙasar nan domin gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa
  • Wani fitaccen malamin addini a jihar Filato, Dakta Isa El-Buba ya jagoranci matasa domin gudanar da zanga zangar a birnin Jos
  • Legit ta tattauna da wani malamin makaranta domin jin ko ya fita zanga zanga kamar yadda wannan malamin ya yi a jihar Filato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Wani fitaccen malamin addinin Kirista mai suna Dakta Isa El-Buba ya jagoranci matasa yin zanga zanga a jihar Filato.

Dakta Isa El-Buba ya bayyana manyan dalilan da suka sanya shi fitowa zanga zangar adawa da tsadar rayuwa duk da yana malamin addini.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a Kano ana daf da fita ta gama gari, bayanai sun fito

Jihar Filato
Malamin addini ya shiga zanga zanga a Filato. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Dakta Isa El-Buba ya fita zanga zangar adawa da tsadar rayuwa tun da sassafe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malami zai jagoranci zanga zanga lafiya

Shahararren mai wa'azin ya ce zanga zangar da ya jagoranta a cikin lafiya da lumana za a yi ta a sassan Filato.

Dakta Isa El-Buba ya tattara matasa ne tun karfe 6 na safe a sakatariyar jihar Filato inda suka nufi hanyar filin jirgin saman jihar.

El-Buba ya fadi dalilin fita zanga zanga

Dakta Isa El-Buba ya ce ya fito zanga zangar ne saboda yadda yan Najeriya ke shan wahala a karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Malamin ya ambaci cire tallafin man fetur, cire tallafin wutar lantarki da tsadar rayuwa a matsayin manyan damuwowin yan Najeriya.

Jami'an tsaro sun yi aiki a Filato

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro su na bin masu zanga zangar a cikin gari domin tabbatar da cewa ba a samu barna ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi, yan sanda sun cafke matashin da ya fito zanga zanga

Wasu masu zanga zangar sun taru a wurare daban daban a jihar Filato ciki har da babban shatale-talen birnin jihar.

Legit ta tattauna da Hamza Adamu

Wani malamin makaranta a jihar Gombe, Hamza Adamu Abdullahi ya bayyanawa Legit cewa shi ba shi da ra'ayin fita zanga zanga saboda rashin tsari.

Hamza Adamu ya ce zai yiwa masu zanga zanga addu'a musamman wanda suka fita cikin tsari a dukkan jihohin Najeriya.

NBA ta goyi bayan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta fitar da sanarwa ta musamman kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Kungiyar NBA ta dauki aniyar ba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa kariya a harkar shari'a idan aka tauye musu hakkinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng