Zanga Zanga: Kungiyar NBA Ta Karfafi Matasa, Ta Daukar Masu Babban Alkawari

Zanga Zanga: Kungiyar NBA Ta Karfafi Matasa, Ta Daukar Masu Babban Alkawari

  • Kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta fitar da sanarwa ta musamman kan masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a ƙasar nan
  • NBA ta dauki aniyar ba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa kariya a harkar shari'a idan aka tauye musu hakkinsu
  • A yau Alhamis ne matasa a fadin Najeriya suka fara fitowa kan tituna domin nuna adawa da tsare-tsaren gwamantin Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta bayyana cewa za ta tallafawa masu zanga zanga a fadin ƙasar nan.

Matakin na zuwa ne bayan matasa sun fita kan tituna domin yin zanga zangar tsadar rayuwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10: Lauya ya nemi alfarma, ya roki masu zanga zanga su rage tsawon lokaci

Zanga zanga
NBA za ta ba masu zanga zanga kariya. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa NBA ta bayyana cewa za ta yi aiki kyauta ne ga duk wanda aka zalunta a lokacin zanga zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NBA za ta taimaki matasa masu zanga zanga

Kakakin kungiyar NBA, Akorede Lawal ya ce za su tsaya ga mutanen da aka tauye wa hakki a lokacin zanga zanga.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Akorede Lawal ya bayyana cewa sun tura umurnin tsayawa masu zanga zanga ga dukkan ofisoshinsu 130 a fadin Najeriya.

NBA za ta sa ido ana zanga zanga

Haka zalika, Akorede Lawal ya ce an ba dukkan ofisoshin NBA umurnin sanya ido a kan yadda zanga zangar za ta gudana.

Ya ce za su duba yadda mu'amala za ta kasance tsakanin jami'an tsaro da al'ummar da suka fito zanga zangar.

NBA ta shawarci masu zanga zanga

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta samu goyon baya daga Amurka, an gargadi Tinubu kan taɓa matasa

Kungiyar NBA ta yi kira ga matasa kan muhimmancin yin zanga-zangar ba tare da jawo tashin hankali ba.

Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa ta rubuta takarda ga sufeton yan sanda kan yadda za su yi aiki tare wajen samar da kwanciyar hankali a lokacin zanga zangar.

NADECO ta goyi bayan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa matasa masu yin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya sun samu goyon baya daga kasar Amurka.

Kungiyar kare martabar dimokuraɗiyya ta NADECO ta reshen Amurka ta gargadi gwamnatin Najeriya kan yunkurin dakile masu zanga zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng