Shinkafar N40,000: Gwamnati Ta Bayyana Lokacin Fara Siyarwa, Ta Fadi Dalilin Boye Buhuna

Shinkafar N40,000: Gwamnati Ta Bayyana Lokacin Fara Siyarwa, Ta Fadi Dalilin Boye Buhuna

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin kin sanar da wuraren siyar da shinkafa mai nauyin kilo 50 kan kudi N40,000 kacal
  • Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka inda ya ce sun dauki matakin ne saboda dalilan tsaro
  • Idris ya kuma ce rashin sanar da wuraren zai taimaka wurin dakile masu siyan shinkafar da yawa domin kuntatawa jama'a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan ce-ce-ku-ce game da shinkafar da ta fitar domin siyarwa a farashin mai rahusa.

Gwamnatin ta ce ta ki bayyana inda ake siyarwa ne saboda ka da wasu masu hali su siya da yawa domin kuntatawa al'umma.

Kara karanta wannan

Ana shirin fita zanga-zanga, matasa sun farmaki mota makare da kayan abinci

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan shinkafar N40,000 da ta fitar
Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin kin fara siyar da shinkafa mai rahusa a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Tinubu ya fadi shirinsa kan shinkafar N40,000

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya bayyana haka a jiya Laraba 31 ga watan Agustan 2024, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce an gama shirya komai domin rarraba shinkafar a jihohi inda ya ce an ki sakin wuraren da ake sayarwa saboda tsaro.

Idris ya kuma ce babban makasudin fitar da shinkafar mai nauyin kilo 50 a kan N40,000 shi ne domin isa wurin wadanda suka fi buƙata, Punch ta tattaro.

Gwamnatin ta shirya rabon shinkafar N40,000

"An shirya komai domin rarraba shinkafar zuwa jihohi, an ki bayyana wuraren da kuma lokaci saboda tsaro amma akwai shinkafar da za a siyar kan N40,000 kacal."
"Ina mai tabbatar muku za a fara siyar da shinkafar a wurare daban-daban na kasar."
"An dauki matakai domin ka da wasu su saye shinkafar da yawa domin su boye wanda hakan zai hana wadanda aka samar da ita dominsu."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

- Mohammed Idris

Inuwa Yahaya ya magantu kan shinkafar Tinubu

Kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce har zuwa yanzu bai karbi tirelar shinkafa daga Gwamnatin Tarayya ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki inda ya yi rantsuwa cewa bai ga ko da buhu daya ba.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ta korafi kan tirelolin shinkafa da Gwamnatin Tarayya ta raba ga gwamnoni a jihohinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.