Ana Fargabar Miyagu Za Su Shiga Zanga Zanga, An Samu Hanyoyi 5 Domin Kare Kai

Ana Fargabar Miyagu Za Su Shiga Zanga Zanga, An Samu Hanyoyi 5 Domin Kare Kai

  • An shiga zanga-zangar kwanaki 10 a dukkanin jihohin Najeriya har da babban birnin tarayya Abuja duk da rokon gwamnati ta rika yi
  • Gwamnati, malamai da sauran manyan 'yan siyasa sun nemi jama'a kar su fita saboda rashin tabbataccen shugabanci a zanga-zangar
  • Rundunar 'yan sanda da sojojin kasar nan sun bayyana cewa sun bankado akwai yiwuwar bata-gari su shiga zanga-zangar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Yayin da aka fara gudanar da zanga-zanga a jihohin kasar nan 36 da babban birnin tarayya Abuja, an shiga fargabar za a iya samun matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10: Lauya ya nemi alfarma, ya roki masu zanga zanga su rage tsawon lokaci

A baya, jami'an tsaro sun yi gargadin cewa akwai fargabar miyagu za su kawo hargitsi tare da tarwatsa zaman lafiyar da ake mora.

Protest
Manyan hanyoyin kare kai a lokacin zanga zanga Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta gano wasu hanyoyi na tabbatar da tsare lafiya da dukiyoyin jama'a a lokacin da za a tsunduma zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Hanyoyin kare kai daga rashin tsaro

Yayin da zanga-zanga ta fara daukar dumi a wasu sassan Najeriya, ciki har da jihar Kano, inda aka fara fashe-hashe a dorayi da ke karamar hukumar Kumbotso, an gano wasu hanyoyin kare kai.

Tsohon kwamandan rundunar tsaro ta JTF, Dr. Isma'ila Tanko Wudilawa ya ce yanzu haka gari ya fara daukar dumi, kuma ya shaidawa Legit yadda ya kamata a kare kara tabarbarewar tsaro;

1. Iyaye su rike yaransu a gida

Dr. Isma'ila Tanko Wudilawa ya ce lokaci ya yi da iyaye za su tabbata dukkanin yaransu na cikin gida.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi abin da ke firgita ta game da zanga zanga

Ya ce ta haka ne za a tabbatar da cewa rikici bai rutsa da matasa da yara - maza da mata sa tashe-tashen hankula ba.

2. Sanya takunkumin fuska wajen zanga-zanga

Masu rashin lafiya kamar cutar numfashi ta Asthma su tabbatar da cewa sun kare lafiyarsu ta hanyar amfani da takunkumin fuska.

Hakan zai kare lafiyar mutane da hana kamuwa da sauran cutuka, da kare su daga shakar iskar borkonon tsohuwa.

3. Ka san dalilin zanga-zanga

Yayin da aka fito tituna domin gudanar da zanga-zanga domin matsin rayuwa da tabbatar da cewa gwamnatin ta saurari koken gwamnati, dole mai fita ya san dalilin fitarsa.

4. Ka san hanyar da za a bi

Ya na da matukar muhimmanci mutum ya san hanyoyin da za a bi yayin gudanar da zanga-zangar lumana domin saurin daukar mataki idan an samu hargitsi.

Ta haka ne mutum zai yi saurin kutsawa ta hanyar domin neman mafaka ba tare da ya illata kansa ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jerin kasuwancin da za su gamu da tangarɗa a lokacin zanga-zanga

5. Ka san jagororin zanga zanga

Akwai bukatar duk wanda zai fita zanga-zanga ya san su waye jagororin zanga-zanga domin sanin su waye za a bi.

Bin jagoranci zai taimaka wajen samun bayanai, da matakan da ya kamata a dauka, kuma su ne za su mika koken ga mahukunta.

Gwamnati ta nemi a dakatar da zanga zanga

A baya kun ji cewa gwamnatin tarayya ta nemi 'yan Najeriya su yi hakuri tare da watsar da batun zanga-zanga saboda matsalar tsaro da hakan zai iya haifarwa.

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ne ya yi kiran, inda ya bayyana cewa an samu bayananan akwai bata gari da za su shiga cikin masu zanga zanga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.