Masu Zanga Zanga Sun Gamu da Cikas a Abuja, Kotu Ta Ba Su Sabon Umarni
- Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, Babbar Kotun Tarayya ta dakile amsu shirin gudanar da ita a gobe Alhamis
- Kotun ta umarci matasan da ke shirin gudanar da zanga-zangar su tsaya iya ka filin wasa na MKO Abiola da ke birnin
- Wannan mataki na kotun na zuwa ne bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shigar da korafi kan shirin da matasan ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan masu shirin zanga-zanga a birnin a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Kotun ta umarci masu zanga-zangar ka da su bazama kan tituna inda tta ba su damar amfani da filin wasa na MKO Abiola.
Kotu ta yi hukunci kan masu zanga-zanga
Alkalin kotun, Mai Shari'a, Sylvanus Orji shi ya yanke hukuncin a yau Laraba 31 ga watan Agustan 2024, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TheCable ta tattaro cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ya shigar da korafi kan shirin zanga-zangar da matasa ke yi a fadin kasar.
Wannan matakin kotun na zuwa ne yayin matasa suka shirya fita zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024.
Zanga-zanga: Wadanda ake kara a gaban kotu
Wadanda ake kara a gaban kotu sun hada da Omoyele Sowore da Damilare Adenola da Adama Ukpabi da Tosin Harsogba.
Sauran sune Sifeta-janar na 'yan sanda da kwamishinan 'yan sanda a Abuja da babban daraktan hukumar DSS.
Sai kuma kwamandan hukumar NSCDC da babban hafsan sojojin kasa da na sama da kuma na ruwa.
Kotu ta yi hukunci kan masu zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun jihar Ogun ta yi hukunci kan korafin da aka shigar kan masu shirin zanga-zanga.
Kotun ta umarci masu zanga-zangar da su gudanar da shirin na su a wurare guda hudu kacal a fadin jihar baki daya.
Wannan na zuwa ne yayin da matasa suka gama shiryawa dmin fita zanga-zanga a gobe Alhamis 1 gaw atan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng