“Ku Rike Gwamnoninku”: Minista Ya Tona Abin Alheri da Tinubu Ya Yi Wa Jihohi
- Yayin da ake shirin fita zanga-zanga a Najeriya, karamin Ministan karafa a kasar, nan Uba Maigari ya roki 'yan Taraba alfarma
- Maigari ya bayyana irin matakan da Bola Tinubu ya dauka domin kawo sauki a tsakanin al'umma duk da halin da ake ciki
- Ministan ya bukaci al'umma su tambayi gwamnoninsu kayan abinci da takin zamani da Gwamnatin Tarayya ta ba su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Karamin Ministan karafa a Najeriya, Uba Maigari ya roki al'ummar jihar Taraba kan fita zanga-zanga da ake shirin yi.
Una Maigari ya ce Shugaba Bola Tinubu ya samar da tsare-tsare masu kyau da za su dakile mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya.
Minista ya fadi matakan da Tinubu ya dauka
Ministan ya bayyana haka ne a Jalingo a jihar Taraba yayin ganawa da masu ruwa da tsaki, Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maigari ya ce daga cikin matakan da Bola Tinubu ya dauka akwai raba kayan abinci da takin zamani ga gwamnoni.
Har ila yau, Maigari ya ce shugaban ya amince da biyan mafi karancin albashi domin ma'aikata.
Abin da Ministan Tinubu ya fadawa mutane
"Shugaba Tinubu ya umarci raba takin zamani da kayan abinci ga gwamnonin jihohi da ke APC da PDP da APGA baki daya.
"Ya kamata a masayinku na 'yan jaridu da masana ku yi aikinku wurin tambayar gwamnoninku musamman ku fara daga nan gida."
"Sauran matakan da Tinubu ya dauka sun hada da karin albashi ga ma'aikata kafin sauran lamuran gwamnatin su amfani jama'a."
- Uba Maigari
Minista ya roki matasa kan zanga-zanga
Maigari ya ce su ma ba su jin dadi yadda ake cikin wahala musamman na karancin abinci wanda shi ne dalilin gwamnatin na daukar matakan.
Ya roki al'ummar jihar Taraba da su guji fita kan tituna domin yin zanga-zanga wanda wasu ne ke son amfani da wannan dama.
'Yan APC sun yi zanga-zanga a Kano
Kun ji cewa daruruwan mutane a jihar Kano sun fito kan tituna inda suke adawa da zanga-zangar da za a yi a ranar Alhamis.
Mutanen sun cika titunan birnin ne a yau Laraba 31 ga watan Agustan 2024 domin nuna rashin goyon baya ga zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng