Ana Saura Kwana 1, Gwamnatin Tinubu Ta Aike da Muhimmin Saƙo Kan Zanga Zanga
- Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya roƙi ƴan Najeriya sun gujewa zanga zangar da aka shirya yi a watan Agusta
- Sanata Akume ya tabbatar wa al'umma cewa wannan wahalar da ake ciki ba za ta dawwama ba, nan gaba kaɗan za a ji daɗi
- Wannan roko na zuwa ne kwana ɗaya kacal gabanin fara zanga-zangar nuna adawa da manufofin gwamnati da suka jawo tsadar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume, ya ƙara fitowa ya roki ‘yan Najeriya da su ƙauracewa zanga-zangar yunwa da ake shirin yi a fadin kasar nan.
Sanata Akume ya yi wannan roko da ake ganin kusan shi ne na ƙarshe gabanin fara zanga-zanga gobe Alhamis a taron manema labarai a Abuja.
Ya ce kwanaki masu cike da alheri na nan tafe kuma nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su samu saukin rayuwa, kamar yadda The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akume ya ce shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana sane da ƴancin yin zanga-zanga amma yana rokon ƴan Najeriya su yi la'akari da halin da ƙasar ke ciki.
Abin da gwamnatin Tinubu take gudu
Ya bayyana cewa babban abin da gwamnati take gudu shi ne, ƴan bindiga, ƴan ta'adda da sauran ƴan tada kayar baya su saje da masu zanga-zangar su yi ɓarna.
George Akume ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, kana su guji duk wasu ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya.
Akume ya ƙara rokon ‘yan Najeriya da su rungumi hanyar zaman lafiya, tattaunawa da haɗin kai, rahoton Channels tv.
Gwamnatin Tinubu ta sake rokon ƴan Najeriya
"Maza da mata, duba da yanayi da nasarorin da muka ambata ina mai sanar da ku cewa Najeriya na kan turbar ci gaba kuma nan ba da daɗewa ba kowa zai gani a ƙasa.
"Wahalhalun da ake fuskanta yanzu haka za su kau nan ba da daɗewa ba, kuma za mu shiga lokacin wadata mara iyaka a ƙasarmu.
"Saboda haka muna kira ga ’yan Najeriya su yi watsi da kiraye-kirayen a fito zanga-zangar adawa da yunwa ta hanyar ba da fifiko ga zaman lafiya da ci gaba."
- George Akume.
Akpabio ya tsokano ƴan zanga-zanga
A wani rahoton kuma, shugaban majalisar dattawa ya tada ƙura, ya tsokani masu shirin fita zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
Sanata Godswill Akpabio ya ce duk wanda ya ga zai fita zanga-zanga ga hanya nan amma su suna can suna cin abinci, ba abin da ya dame su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng