"Kifar da Gwamnati Zai Tarwatsa Najeriya" Sheikh Gumi Ya Fadi Hadarin Juyin Juya Hali
- Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya kara kira ga matasa masu shirin zanga-zanga a kasar nan
- Malamin wanda da farko ya goyi bayan zanga-zanga ya sauya ra'ayi, inda ya hango babban illar da ke tattare da bore ga gwamnati
- A wani karatunsa, Sheikh Gumi ya bayyana cewa akwai hadari idan aka kifar da gwamnati ba ta hanyar gudanar da zabe ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya sabunta kira ga 'yan Najeriya a kan kokarin bore ga gwamnati.
A wani karatun malamin, ya bayyana cewa kifar da gwamnati ta hanyar amfani da karfi zai jawo gagarumar matsala a Najeriya.
A wani bidiyon da Mu'ammar Gaddaf ya wallafa a shafinsa na X, Sheikh Gumi ya ce za a samu bullar kungiyoyin 'yan bindiga bila adadin a fadin kasar idan aka girgide gwamnati da karfin tsiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sojoji ba za su iya mulki ba," Sheikh Gumi
Shahararren malamin addinin, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya ce an samu rarrabuwar kai a rundunar sojojin kasar nan.
Saboda haka ne ya ke ganin ko an kifar da gwamnati, ba za su iya mulkin Najeriya ba.
"In ka kifar da gwamnati na tsarin zabe, to wace irin gwamnati za ka zo da ita?"
- Dr. Ahmad Mahmud Gumi
Malamin ya kara da cewa yan ta'adda da masu rike da bindiga sun yi yawa a Najeriya, inda ya ce za su kawo tarnaki da zarar an kifar da gwamnati.
Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya ce 'yan ta'adda irinsu IPOB, Boko Haram da masu garkuwa da mutane na daga cikin manyan matsalolin da za su yi ƙamari.
Zanga-zanga: Sheikh Gumi ya sauya matsaya
A baya mun wallafa cewa malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi ya dawo daga ra'ayinsa na a tafi zanga-zanga, ya sake matsaya.
A sabon kiran da ya yi ga matasa, ya shawarce su da kar su shiga zanga-zangar saboda babu tsayayyen shugabanci, wanda hakan babbar barazana ce ga tafiyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng