Matasa Sun Yi Wa Sanata Akpabio Rubdugu Bayan Tsokano Masu Zanga Zanga

Matasa Sun Yi Wa Sanata Akpabio Rubdugu Bayan Tsokano Masu Zanga Zanga

  • Matasan Najeriya sun dura kan shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Obot Akpabio kan maganganun da ya musu
  • Sanata Godswill Akpabio ya shiga tarkon matasan Najeriya ne bayan magana da ya yi a kan zanga zanga da ta bata musu rai
  • Da yawa daga cikin matasan Najeriya sun nuna rashin dacewarsa da rike matsayin shugaban majalisar dattawa a kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da ake shirin fara zanga zangar tsadar rayuwa a Najeriya shugaban majalisar dattawa ya fusata matasan Najeriya.

Sanata Godswill Akpabio ya yi magana ne a kan zanga zangar adawa da tsadar rayuwa da matasan ke shirin farawa.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi, yan sanda sun cafke matashin da ya fito zanga zanga

Sanata Akpabio
Matasa sun fusata bayan maganar Sanata Akpabio. Hoto: @SPNigeria
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro wasu zafafan martani da matasan Najeriya suka yi wa shugaban majalisar dattawan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar da Godswill Akpabio ya yi

Legit ta ruwaito cewa a yayin wani taro a jihar Rivers, Godswill Akpabio ya ce kowa yana shan wahala a Najeriya amma sun san komai zai wuce.

Saboda haka ya ce masu zanga zanga su yi ta fama amma su kam za su samu wuri su rika cin abinci wanda hakan ya bata ran matasan Najeriya.

"A yi wa Sanata Akpabio kiranye"

Wani mai amfani da kafar X @kafeel_maje1 ya bukaci matasa su tilasta yiwa Sanata Akpabio ritaya.

Matashin ya ce hakan abu mai yiwuwa ne matukar matasan Najeriya za su sa kwazo kan lamarin.

"Akpabio bai dace da mukamin majalisa ba?"

Wani mai amfani da kafar Facebook Isaiah Jeremiah ya ce haka ne zai rika faruwa matuƙar wadanda basu cancanta ba suna rike shugabanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ka samar mana da motoci": Masu zanga zanga sun tura bukatunsu ga gwamna

Abubakar Sadiq Adamu ya ce Akpabio shi ne mafi rashin dacewa a cikin shugabannin majalisar dattawa da aka yi a Najeriya.

Zanga zanga: Sanata Akpabio ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, ya bayyana wadanda ke da hannu wajen daukar nauyin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Godswill Akpabio ya ce 'yan siyasar da suka gaza cimma manufarsu a lokacin babban zaben 2023 ne ke da hannu a zanga-zangar adawa da Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng