Atiku Ya Raina Dabarun Tinubu Bayan Jin Yunwa ta Rutsa Yaran Najeriya Miliyan 4.4

Atiku Ya Raina Dabarun Tinubu Bayan Jin Yunwa ta Rutsa Yaran Najeriya Miliyan 4.4

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin yadda ake samun ƙaruwar yunwa a Najeriya
  • Atiku Abubakar ya bayyana bacin ransa ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa, inda ya ce dole ne a nemo mafita
  • Atiku, wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne a jami'yyar PDP ya ce lokaci ya yi na daukar batun magance yunwa da gaske

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana kaɗuwa bisa yadda ake samun ƙaruwar yunwa a ƙasar nan.

Ya ce akwai takaici matuƙa a kan alkaluman da shirin samar da abinci na duniya su ka nuna cewa miliyoyin yaran kasar nan na fama da yunwa.

Kara karanta wannan

"Muna can muna cin abinci," Shugaban Majalisa ya ta da ƙura kan zanga zanga da ake shirin yi

Atiku
Atiku Abubakar ya shiga takaicin yunwa a Najeriya Hoto: AbdulRasheeth Shehu
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya ce yanzu haka alkaluma sun nuna cewa akalla yara miliyan 4.4 ne ke cikin yunwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnati ta magance yunwa" - Atiku Abubakar

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnatoci a mataki daban-daban za su magance yunwa.

A sakon da tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce bayar da tallafin abinci ba zai magance yunwar da ta rutsa kasar nan ba.

Atiku ya fadi hanyoyin magance yunwa

Atiku Abubakar ya ce daga cikin hanyoyin da gwamnati za ta iya dauka na magance yunwa akwai karfafa tsaro, daidaitawa da hana hauhawar farashin abinci.

Sauran hanyoyin da tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana sun hada da neman shawarar kwararru a fannin noma da tallafawa manoma.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Villa kwanaki 3 gabanin fara zanga zanga

Atiku Abubakar ya magantu kan zanga-zanga

A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce 'yan Najeriya na da 'yancin gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar ya ce wadanda ke son hana gudanar da zanga-zanga a yanzu sun jagoranci gudanar da ita a shekarun baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.