Awanni Kafin Fita Tituna, APC a Kano Ta Roki Matasa Alfarma Kan Lamarin Zanga Zanga
- Yayin da ake shirin shiga zanga-zanga a Najeriya, jigon jam'iyyar APC a Kano ya roki 'yan jihar ka da su fita kan tituna
- Nasiru Bala Ja'oji ya ce tabbas wasu kasasehen Afirka sun shiga mummunan yanayi saboda zanga-zanga a aka fara
- Ja'oji ya ce kuma sun sani ana shan wahala a Najeriya amma fa ba a lokacin mulkin Bola Tinubu aka fara fuskantar haka ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Jigon jam'iyyar APC a jihar Kano ya roki 'yan jihar da su guji fitowa zanga-zanga da ake shirin yi a fadin kasar.
Nasiru Bala Ja'oji ya ce nuna damuwa kan tsare-tsaren gwamnati ba matsala ba ne amma ta hanyar rigima bai kamata ba.
Zanga-zanga: Jigon APC ya roki 'yan Kano
Ja'oji ya bayyana haka ne a taron manema labarai da 'ya'yan jam'iyyar APC da shugabannin mata, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wahalar da ake ciki yanzu ba a mulkin Shugaba Bola Tinubu aka fara ba inda ya ce shugaban ya dauki aniyar kawo sauki a kasa.
Har ila yau, Ja'oji ya ce Tinubu mutum ne mai jin koke-koken 'yan kasa inda ya tabbatar da cewa komai zai dawo dai-dai a kasar.
APC ta kare Tinubu kan halin kunci
"Wahalar da ake ciki ba a gwamnatin Tinubu aka fara ba, tabbas akwai kunci a kasa, Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin komai zai daidaita."
"Samun zaman lafiya da hadin kai a kasa shi ne babban abin da muke bukata a Najeriya, wasu kasashen Afirka sun shiga matsala kan zanga-zanga."
"Kasashen sun shiga matsala ne bayan wasu miyagu sun shiga cikinsu yayin zanga-zanga inda suka kawo matsala."
- Bala Ja'oji
Matasa sun fasa motar abinci a Najeriya
Kun ji cewa wasu matasa sun farmaki babbar motar bas makare da kayan abinci a jihar Cross River inda suka raunata da dama.
Motar dauke da kayan abinci a cike ta nufi sakatariyar kungiyar 'yan jaridu ne a jihar domin rabon tallafi ga mambobinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng